Filemon
1
Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu,
 
Zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu, zuwa kuma ga Affiya ’yar’uwarmu, zuwa kuma ga Arkiffus abokin famarmu, da zuwa kuma ga ikkilisiyar da take taruwa a gidanka.
 
Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.
 
Godiya da addu’a
Kullum nakan gode wa Allahna sa’ad da nake tuna da kai cikin addu’o’ina, domin ina jin labari bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunarka da kake yi saboda dukan tsarkaka. Ina addu’a ka zama mai ƙwazo cikin shaida bangaskiyarka, domin ka sami cikakken fahimta ta kowane abin da yake nagarin da muke da shi cikin Kiristi. Ƙaunarka ta sa ni farin ciki ƙwarai ta kuma ƙarfafa ni, domin kai, ɗan’uwa, ka wartsake zukatan tsarkaka.
Roƙon Bulus domin Onisemus
Saboda haka, ko da yake cikin Kiristi ina iya yin ƙarfin hali in umarce ka ka yi abin da ya kamata, duk da haka ina roƙonka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Kiristi Yesu. 10 Ina roƙonka saboda ɗana Onesimus,* Onesimus yana nufin mai amfani. wanda ya zama ɗana yayinda nake cikin sarƙoƙi. 11 Dā kam, ba shi da amfani a gare ka, amma yanzu ya zama da amfani a gare ka da kuma gare ni.
12 Ina aike shi yă koma gare ka, shi da yake zuciyata. 13 Na so in riƙe shi a wurina a madadinka domin yă taimake ni yayinda nake cikin sarƙoƙi saboda bishara. 14 Sai dai ban so in yi kome ban da yardarka ba, domin kowane alherin da za ka yi, yă fito daga zuciyarka, ba na tilas ba. 15 Wataƙila abin da ya sa aka raba ka da shi na ɗan lokaci ƙanƙani shi ne don ka same shi da amfani 16 ba kamar bawa kuma ba, sai dai fiye da bawa, a matsayin ƙaunataccen ɗan’uwa. Shi ƙaunatacce ne sosai a gare ni amma a gare ka ya ma fi zama ƙaunatacce, kamar mutum da kuma kamar ɗan’uwa a cikin Ubangiji.
17 Saboda haka in ka ɗauke ni a kan ni abokin tarayya ne, sai ka marabce shi kamar yadda za ka marabce ni. 18 In ya yi maka wani laifi ko kuma yana riƙe maka wani bashi, sai ka mai da shi a kaina. 19 Ni, Bulus, nake rubuta wannan da hannuna. Zan biya ka, kada ma a yi zancen ranka da kake riƙe mini bashi. 20 Ina fata, ɗan’uwa, zan sami amfani daga gare ka cikin Ubangiji; ka wartsake zuciyata cikin Kiristi. 21 Da tabbacin biyayyarka, ina rubuta maka, da sanin za ka yi fiye da abin da na ce.
22 Abu guda ya rage, ka shirya mini masauƙi, domin ina bege za a mayar da ni gare ku albarkacin addu’o’inku.
 
 
23 Efafaras, abokin tarayyata a kurkuku cikin Kiristi Yesu, yana gaishe ka.
24 Haka kuma Markus, Aristarkus, Demas da kuma Luka, abokan aikina.
 
25 Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku.

*1:10 Onesimus yana nufin mai amfani.