2
Koyi tawali’un Kiristi
In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi, to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa. Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku. Bai kamata kowannenku yă kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai yă kula da sha’anin waɗansu ma.
A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.
Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake,
bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,
amma ya mai da kansa ba kome ba,
yana ɗaukan ainihin surar bawa,
aka yi shi cikin siffar mutum.
Aka kuma same shi a kamannin mutum,
ya ƙasƙantar da kansa
ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa,
mutuwar ma ta gicciye!
 
Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri
ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,
10 don a sunan Yesu kowace gwiwa za tă durƙusa,
a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa,
11 kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne,
don ɗaukakar Allah Uba.
Haskaka kamar taurari
12 Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki, 13 gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.
14 Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba, 15 don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya 16 kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba. 17 Amma ko da ana tsiyaye jinina kamar hadaya ta sha a kan hadaya da kuma hidimar da take fitowa daga bangaskiyarku, ina murna ina kuma farin ciki da ku duka. 18 Haka ma ya kamata ku yi murna ku kuma yi farin ciki tare da ni.
Timoti da Afaforiditus
19 Ina sa rai a cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika da Timoti zuwa gare ku ba da daɗewa ba, don ni ma in ji daɗi sa’ad da na ji labarinku. 20 Ba ni da wani kamar sa, wanda yake da ainihin sha’awa a zaman lafiyarku. 21 Gama kowa yana lura da al’amuran kansa ne kawai, ba na Kiristi Yesu ba. 22 Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa. 23 Saboda haka, ina sa rai, in aike shi da zarar na ga yadda abubuwa suke a nan. 24 Ni kuma ina da tabbaci a cikin Ubangiji cewa zan zo ba da daɗewa ba.
25 Amma ina gani ya dace in aika da Afaforiditus, ɗan’uwana, abokin aikina da kuma abokin famana, wanda kuma yake ɗan saƙonku, wanda kuka aika domin yă biya mini bukatuna. 26 Gama yana marmarin ganinku duka ya kuma damu domin kun ji cewa ya yi rashin lafiya. 27 Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don yă rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki. 28 Saboda haka na yi niyya ƙwarai in aike shi wurinku, don sa’ad da kuka sāke ganinsa za ku yi murna, ni kuma in rage damuwa. 29 Ku marabce shi cikin Ubangiji da farin ciki mai yawa, ku kuma girmama mutane irinsa, 30 domin ya kusa yă mutu saboda aikin Kiristi, ya yi kasai da ransa don yă cikasa taimakon da ba ku iya yi mini ba.