2
Ribar ɗa’ar hikima
Ɗana, in ka yarda da kalmomina
ka kuma ajiye umarnaina a cikinka,
kana kasa kunne ga abin da yake na hikima,
kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi,
in kuma ka kira ga tsinkaya
ka kuma kira da ƙarfi don ganewa,
in ka neme shi yadda ake neman azurfa
ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya,
to, za ka gane tsoron Ubangiji
ka kuma sami sanin Allah.
Gama Ubangiji yana ba da hikima,
daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.
Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya,
shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi,
gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata
yana kuma tsare hanyar amintattunsa.
 
Sa’an nan za ku fahimci abin da yake daidai da abin da yake na adalci
da abin da yake gaskiya, da kowace hanya mai kyau.
10 Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka,
sani kuma zai faranta maka rai.
11 Tsinkaya za tă tsare ka,
ganewa kuma za tă yi maka jagora.
 
12 Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane,
daga kalmomin mutane masu ɓatanci,
13 waɗanda suke barin miƙaƙƙun hanyoyi
don su yi tafiya a hanyoyi masu duhu,
14 waɗanda suke jin daɗin yin abin da ba shi da kyau
suna kuma farin ciki a mugayen ɓatanci,
15 waɗanda hanyoyinsu karkatattu ne
waɗanda kuma suke cuku-cuku a hanyoyinsu.
 
16 Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya,
daga mace mai lalata, mai ƙoƙarin kama ka da daɗin bakinta,
17 wadda ta bar mijin ƙuruciyarta
ta kuma ƙyale alkawarin da ta yi a gaban Allah.*Ko kuwa alkawarin Allahnta
18 Gama gidanta yana kai ga mutuwa
hanyarta kuma ga ruhohin matattu.
19 Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa
ba zai ƙara komowa ga hanyar rai.
 
20 Don haka dole ku yi tafiya a hanyoyin mutanen kirki
ku kuma yi ta bi hanyoyin adalai.
21 Gama masu aikata gaskiya za su zauna a cikin ƙasar,
marasa laifi kuma za su kasance a cikinta;
22 amma za a fid da mugaye daga ƙasar,
za a tumɓuke marasa aminci kuma daga gare ta.

*2:17 Ko kuwa alkawarin Allahnta