12
Duk mai ƙaunar horo yana ƙaunar sani,
amma duk mai ƙin gyara wawa ne.
 
Mutumin kirki kan sami tagomashi daga Ubangiji,
amma Ubangiji yakan hukunta mai son yin wayo.
 
Ba yadda mutum zai kahu ta wurin aikata mugunta,
amma ba za a tumɓuke adali ba.
 
Mace mai halin kirki rawanin mijinta ne,
amma mace marar kunya tana kama da ciwo a ƙasusuwansa.
 
Shirye-shiryen masu adalci daidai ne,
amma shawarar mugaye ruɗu ne.
 
Kalmomin mugu sukan kwanta suna jira su yi kisankai,
amma jawabin masu aikata gaskiya kan kuɓutar da su.
 
Akan tumɓuke mugaye ba a ƙara ganinsu,
amma gidan masu adalci kan tsaya daram.
 
Akan yabi mutum bisa ga hikimarsa,
amma mutane marasa azanci akan rena su.
 
Gara ka zama kai ba kome ba ne amma kana da bawa
da ka mai da kanka kai wani ne alhali kuwa ba ka da abinci.
 
10 Mai adalci kan kula da bukatun dabbobinsa,
amma halaye mafi kyau na mugaye su ne ƙeta.
 
11 Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace,
amma shi da yake naushin iska marar azanci ne.
 
12 Mugaye suna sha’awar ganimar mugayen mutane,
amma saiwar masu adalci kan haɓaka.
 
13 Mugun mutum kan fāɗa a tarkon maganarsa ta zunubi,
amma adali kan kuɓuta daga wahala.
 
14 Daga abubuwan da suke fitowa daga leɓunansa mutum kan cika da abubuwa masu kyau
tabbatacce yadda aikin hannuwansa suke ba shi lada.
 
15 Hanyar wawa daidai take a gare shi,
amma mai hikima kan saurari shawara.
 
16 Wawa kan nuna fushinsa nan take,
amma mai la’akari kan ƙyale zargi.
 
17 Mashaidin gaskiya kan ba da shaidar gaskiya,
amma mashaidin ƙarya yana baza ƙarairayi ne.
 
18 Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi,
amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa.
 
19 Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada,
amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai.
 
20 Akwai ruɗu a zukatan waɗanda suke ƙulla mugunta,
amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki.
 
21 Ba wani lahanin da zai sami masu adalci,
amma mugaye suna da nasu cike da wahala.
 
22 Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya,
amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.
 
23 Mai la’akari kan kiyaye saninsa wa kansa,
amma zuciyar wawa kan yi ta tallar wawanci.
 
24 Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki,
amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta.
 
25 Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum,
amma maganar alheri kan faranta masa rai.
 
26 Adali yakan yi hankali a abokantaka,
amma hanyar mugaye kan kai su ga kaucewa.
 
27 Rago ba ya gashin abin da ya kama daga farauta,
amma mai aiki tuƙuru yakan ɗauki mallakarsa da muhimmanci.
 
28 A hanyar adalci akwai rai;
a wannan hanya akwai rashin mutuwa.