Zabura
LITTAFI NA ƊAYA
1
Zabura 1–41
Mai farin ciki ne mutumin
da ba ya aiki da shawarar mugaye
ko yă yi abin da masu zunubi suke yi
ko yă zauna tare da masu yin ba’a.
Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji,
kuma yana ta nazarinta dare da rana.
Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa,
wanda yake ba da amfani a daidai lokaci
wanda kuma ganyensa ba sa bushewa.
Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.
 
Ba haka yake da mugaye ba!
Su kamar yayi ne
da iska take kwashewa.
Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba,
balle a sami masu zunubi a taron adalai.
 
Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa,
amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.