Zabura 4
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda.
1 Ka amsa mini sa’ad da na kira gare ka,
Ya Allahna mai adalci.
Ka ba ni sauƙi daga wahalata;
ka ji tausayina ka kuma ji addu’ata.
2 Har yaushe, ya ku mutane za ku mai da ɗaukakata abin kunya?
Har yaushe za ku ƙaunaci ruɗu ku nemi allolin ƙarya?
Sela
3 Ku san cewa Ubangiji ya keɓe masu tsoron Allah wa kansa;
Ubangiji zai ji sa’ad da na yi kira gare shi.
4 Cikin fushinku kada ku yi zunubi;
sa’ad da kuke kan gadajenku,
ku bincike zukatanku ku kuma yi shiru.
Sela
5 Ku miƙa hadayun da suka dace
ku kuma dogara ga Ubangiji.
6 Yawanci suna cewa, “Wa zai yi mana alheri?”
Bari hasken fuskarka yă haskaka a kanmu, ya Ubangiji.
7 Ka cika zuciyata da farin ciki
sa’ad da hatsinsu da sabon ruwan inabinsu ya yi yawa.
8 Zan kwanta in kuma yi barci lafiya,
gama kai kaɗai, ya Ubangiji,
kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.