Zabura 6
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Bisa ga sheminit.*mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce. Ta Dawuda.
Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka
ko ka hore ni cikin hasalarka.
Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma;
Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo.
Raina yana cikin wahala.
Har yaushe, ya Ubangiji, har yaushe?
 
Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni;
ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka.
Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu.
Wa ke yabonka daga kabari?Da Ibraniyanci Sheol
 
Na gaji tiƙis daga nishi.
 
Dukan dare na jiƙe gadona da kuka
na jiƙe kujerata da hawaye.
Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki;
sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana.
 
Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta,
gama Ubangiji ya ji kukata.
Ubangiji ya ji kukata saboda jinƙansa;
Ubangiji ya karɓi addu’ata.
10 Dukan abokan gābana za su sha kunya su kuma karaya;
za su juya da kunya nan da nan.

*^ mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce.

Zabura 6:5 Da Ibraniyanci Sheol