Zabura 8
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit.*Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce. Zabura ta Dawuda.
1 Ya Ubangiji, shugabanmu,
sunanka da girma take a cikin dukan duniya!
Ka kafa ɗaukakarka
bisa sammai.
2 Daga leɓunan yara da jarirai
ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka
da masu ɗaukan fansa su yi shiru.
3 Sa’ad da na dubi sammai,
aikin yatsotsinka,
wata da taurari
waɗanda ka ajiye a wurarensu,
4 wane ne mutum da kake tunawa da shi,
ɗan mutum da kake lura da shi?
5 Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah†Ko kuwa da rayayyun sama
ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.
6 Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka;
ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,
7 dukan shanu da tumaki,
da kuma namun jeji,
8 tsuntsayen sararin sama
da kifin teku,
da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.
9 Ya Ubangiji, shugabanmu,
sunanka da girma take a cikin dukan duniya!