Zabura 14
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda.
1 Wawaye sukan ce a ransu,
“Ba Allah.”
Sun lalace, ayyukansu kuwa mugaye ne;
babu wani da yake yi abu mai kyau.
2 Ubangiji ya duba daga sama
a kan ’yan adam
don yă ga ko akwai wani da ya gane,
wani wanda yake neman Allah.
3 Duka sun kauce, duka gaba ɗaya sun zama lalatattu;
babu ɗaya wanda yake yin abu mai kyau,
ba ko ɗaya.
4 Masu aikata mugunta za su taɓa koyo.
Suna cin mutane yadda mutane ke cin gurasa
kuma waɗanda ba sa kira bisa Ubangiji?
5 Ga su, tsoro ya sha kansu,
gama Allah yana cikin ƙungiyar adalai.
6 Ku masu mugunta kuna sa ƙoƙarin matalauta yă zama banza,
amma Ubangiji ne mafakansu.
7 Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana!
Sa’ad da Ubangiji zai maido da sa’ar mutanensa,
bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna!