Zabura 19
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
1 Sammai suna shelar ɗaukakar Allah;
sararin sama suna furta aikin hannuwansa.
2 Kowace rana tana yin jawabi;
kowane dare yana nuna sani.
3 Ba magana, ba kalmar da aka hurta,
ba wani amon da aka ji daga gare su.
4 Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya,
kalmominsu zuwa iyakokin duniya.
A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,
5 wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa,
kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yă yi tsere.
6 Takan taso daga ƙarshen sammai
ta kewaye zuwa wancan;
babu abin da yake ɓuya wa zafinta.
7 Dokar Ubangiji cikakkiya ce,
takan wartsakar da rai.
Farillan Ubangiji abin dogara ne,
suna mai da hikima da sauƙi.
8 Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne,
suna ba da farin ciki ga zuciya.
Umarnan Ubangiji haske ne
suna ba da haske ga idanu.
9 Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya,
zai kasance har abada.
Farillan Ubangiji tabbatattu ne,
kuma gaba ɗaya masu adalci ne.
10 Sun fi zinariya daraja,
fiye da zalla zinariya nesa;
sun fi zuma zaƙi
fiye da zuma daga kaki.
11 Ta wurinsu ana gargaɗe bawanka;
a kiyaye su akwai lada mai girma.
12 Wane ne zai iya rabe kurakuransa?
Ya gafarta ɓoyayyun laifofinsa.
13 Ka kiyaye bawanka daga zunubin ganganci;
kada ka bari su yi mulki a kaina.
Ta haka zan zama marar laifi;
marar laifi na babban tawaye.
14 Bari kalmomin bakina da tunanin zuciyata
su zama abin gamsuwa a gabanka,
Ya Ubangiji, Dutsena da Mai fansata.