Zabura 24
Zabura ta Dawuda.
1 Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta,
duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta;
2 gama ya gina ta a kan tekuna
ya kafa ta a kan ruwaye.
3 Wa zai iya hawan tudun Ubangiji?
Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?
4 Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya,
wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki
ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.
5 Zai sami albarka daga Ubangiji
da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.
6 Irin tsaran waɗanda suke nemansa ke nan,
waɗanda suke neman fuskarka, ya Allah na Yaƙub.
Sela
7 Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi;
ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi,
don Sarkin ɗaukaka yă shiga.
8 Wane ne wannan Sarkin ɗaukaka?
Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko,
Ubangiji mai girma a yaƙi.
9 Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi;
ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi,
don Sarkin ɗaukaka yă shiga.
10 Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka?
Ubangiji Maɗaukaki,
shi ne Sarkin ɗaukaka.
Sela