Zabura 26
Ta Dawuda.
1 Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji,
gama na yi rayuwa marar zargi;
Na dogara ga Ubangiji
ba tare da kaucewa ba.
2 Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni,
ka bincike zuciyata da tunanina;
3 gama ƙaunarka kullum tana a gabana,
kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka.
4 Ba na zama tare da masu ruɗu,
ko in yi tarayya da masu riya;
5 na ƙi jinin taron masu aikata mugunta
na ƙi in zauna tare da mugaye.
6 Na wanke hannuwana cikin rashin laifi,
ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji,
7 ina shelar yabonka da ƙarfi
ina faɗin dukan ayyukanka masu banmamaki.
8 Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji,
wurin da ɗaukakarka ke zaune.
9 Kada ka ɗauke raina tare da masu zunubi
raina tare da masu son yin kisankai
10 waɗanda akwai mugayen dabaru a hannuwansu,
waɗanda hannuwansu na dama suna cike da cin hanci.
11 Amma na yi rayuwa marar zargi;
ka cece ni ka kuma yi mini jinƙai.
12 Ƙafafuna suna tsaye daram;
cikin taro mai girma zan yabi Ubangiji.