*Wannan zabura waƙa ce, mai ayoyin da suka fara da harufan Ibraniyanci bi da bi.
Zabura 37
Ta Dawuda.
Kada ka tsorata saboda mugayen mutane
ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta;
gama kamar ciyawa za su bushe,
kamar ɗanyun ganyaye za su mutu.
 
Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri;
yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.
Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji
zai kuwa biya bukatun zuciyarka.
 
Ka sa kanka a hanyar Ubangiji;
ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.
Zai sa adalcinka yă haskaka kamar hasken safiya,
gaskiyarka kuma kamar rana a tsaka.
 
Ka natsu a gaban Ubangiji
ka kuma jira da haƙuri gare shi;
kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu,
sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.
 
Kada ka yi fushi kada kuma ka yi hasala;
kada ka tsorata, wannan yakan kai ga mugunta ne kawai.
Gama za a datse mugayen mutane,
amma waɗanda suke sa zuciya ga Ubangiji za su gāji ƙasar.
 
10 A ɗan ƙanƙanen lokaci, mugaye za su shuɗe;
ko ka neme su, ba za a same su ba.
11 Amma masu tawali’u za su gāji ƙasar
su kuma zauna da cikakkiyar salama.
 
12 Mugaye sukan shirya wa adalai maƙarƙashiya
su ciji baki a kansu;
13 amma Ubangiji yakan yi dariyar mugaye,
gama ya sani ranarsu tana zuwa.
 
14 Mugaye sukan zare takobi
su ja baka
don su kashe matalauta da masu bukata,
don su kashe waɗanda hanyoyinsu daidai suke.
15 Amma takubansu za su soki zukatansu,
kuma bakkunansu za su kakkarye.
 
16 Ƙanƙanen abin da mai adalci yake da shi
ya fi arzikin mugaye yawa;
17 gama za a kakkarya ikon mugaye,
amma Ubangiji zai riƙe mai adalci.
 
18 Kwanakin marasa zarge suna sane ga Ubangiji,
kuma gādonsu zai dawwama har abada.
19 A lokutan masifu ba za su yanƙwane ba;
a kwanakin yunwa za su sami a yalwace.
 
20 Amma mugaye za su hallaka,
Abokan gāban Ubangiji za su zama kamar kyan gonaki,
za su ɓace, za su ɓace kamar hayaƙi.
 
21 Mugaye kan yi rance ba sa kuma biya,
amma masu adalci suna bayar hannu sake;
22 waɗanda Ubangiji ya sa wa albarka za su gāji ƙasar,
amma waɗanda ya la’anta, za a kore su.
 
23 In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi,
zai sa sawu su kahu;
24 ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba,
gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa.
 
25 Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa,
duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba
ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi.
26 Kullum suna bayar hannu sake suna kuma ba da bashi ba da wahala ba,
za a yi wa ’ya’yansu albarka.
 
27 Ku juyo daga mugunta ku yi alheri;
sa’an nan za ku zauna a ƙasar har abada.
28 Gama Ubangiji yana ƙaunar masu aikata daidai
kuma ba zai yashe amintattunsa ba.
 
Za a hallaka masu aikata mugunta gaba ɗaya,
’ya’yan mugaye za su hallaka.
29 Masu adalci za su gāji ƙasar
su kuma zauna a cikinta har abada.
 
30 Bakin mutum mai adalci yakan yi magana da hikima,
harshensa kuwa yakan yi maganar abin da yake daidai.
31 Dokar Allahnsa tana a cikin zuciyarsa;
ƙafafunsa ba sa santsi.
 
32 Mugaye suna fako suna jira masu adalci,
suna ƙoƙari neman ransu;
33 amma Ubangiji ba zai bar su a ikonsu ba
ko ya bari a hukunta su sa’ad da aka kawo su shari’a ba.
 
34 Ku sa zuciya ga Ubangiji
ku kuma kiyaye hanyarsa.
Zai ɗaukaka ku ku ci gādon ƙasar,
sa’ad da aka kawar da mugaye, za ka gani.
 
35 Na ga wani mugu, azzalumi,
yana yaɗuwa kamar ɗanyen itace a asalin ƙasarsa,
36 amma yakan mutu nan da nan kuma ba ya ƙara kasancewa;
ko an neme shi, ba za a same shi ba.
 
37 Ka dubi marasa zargi, ka lura da adali;
akwai sa zuciya domin mutum mai salama.
38 Amma za a hallaka dukan masu zunubi;
za a yanke sa zuciya ta mugaye.
 
39 Ceton adalai kan zo daga Ubangiji;
shi ne mafaka a lokacin wahala.
40 Ubangiji yakan taimake su yă kuma cece su;
yakan kuɓutar da su daga mugaye yă kuma cece su,
domin sukan nemi mafaka daga gare shi.

*^ Wannan zabura waƙa ce, mai ayoyin da suka fara da harufan Ibraniyanci bi da bi.