Zabura 53
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat.*Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Wani maskil†Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. na Dawuda.
1 Wawa ne kawai yakan ce a zuciyarsa,
“Ba Allah.”
Sun lalace, kuma hanyoyinsu ba su da kyau;
babu wani mai aikata abu mai kyau.
2 Allah yana duba daga sama
a kan ’ya’yan mutane
yă ga ko akwai wani wanda ya gane,
wani wanda yake neman Allah.
3 Kowa ya kauce, gaba ɗaya sun lalace;
babu guda da yake aikata abu mai kyau,
babu ko ɗaya.
4 Masu aikata mugunta ba sa taɓa koyo?
Suna cin mutanena kamar yadda ake cin burodi,
ba sa kuma kira ga Allah.
5 Ga shi fa, sun firgita don tsoro,
ko da yake babu dalilin tsoro,
gama Allah zai watsar da ƙasusuwan masu ƙinsa,
za su sha kunya, gama Allah ya ƙi su.
6 Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana!
Sa’ad da Allah ya sāke arzuta mutanensa,
bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna!