Zabura 59
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam.*Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Sa’ad da Shawulu ya aiki mutane su yi tsaron gidan Dawuda don yă kashe shi.
Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah;
ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini.
Ka kuɓutar da ni daga masu aikata mugunta
ka kuma cece ni daga masu kisa.
 
Duba yadda suka kwanta suna jirana!
Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni
ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji.
Ban yi wani laifi ba, duk da haka suna a shirye su fāɗa mini.
Tashi ka taimake ni; dubi halin da nake ciki!
Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki,
Allah na Isra’ila,
ka tashi ka hukunta dukan al’ummai;
kada ka nuna jinƙai ga mugaye maciya amana.
Sela
 
Sukan dawo da yamma,
suna wage haƙora kamar karnuka,
suna yawo a birni.
Dubi abin da suke tofawa daga bakunansu,
suna tofar da takuba daga leɓunansu,
suna cewa, “Wa zai ji mu?”
Amma kai, ya Ubangiji, kakan yi musu dariya;
kana yi wa dukan waɗannan al’ummai ba’a.
 
Ya ƙarfina, na dogara gare ka;
kai, ya Allah, kai ne kagarata, 10 Allah mai ƙaunata.
 
Allah zai sha gabana
zai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina.
11 Amma kada ka kashe su, ya Ubangiji garkuwarmu,
in ba haka mutanena za su manta.
Cikin ikonka ka sa su yi ta yawo barkatai,
ka kuma kawar da su.
12 Saboda zunuban bakunansu,
saboda maganganun leɓunansu,
bari a kama su cikin fariyarsu.
Saboda zage-zage da ƙarairayin da suke yi,
13 ka cinye su da hasala,
ka cinye su sarai.
Sa’an nan za a sani a iyakar duniya
cewa Allah yana mulki a bisa Yaƙub.
Sela
 
14 Sukan dawo da yamma,
suna wage haƙora kamar karnuka,
suna yawo a birni.
15 Suna ta yawo neman abinci
su kuwa yi haushi in ba su ƙoshi ba.
16 Amma zan rera game da ƙarfinka,
da safe zan rera game da ƙaunarka;
gama kai ne mafakata,
kagarata a lokacin wahala.
 
17 Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka;
kai, ya Allah, kai ne kagarata,
Allah mai ƙaunata.

*^ Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.