Zabura 64
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
1 Ka ji ni, ya Allah, yayinda nake faɗin abin da yake damuna;
ka tsare raina daga barazanan abokin gāba.
2 Ka ɓoye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye,
daga daure dauren wannan taro masu aikata mugunta.
3 Sukan wāsa harsunansu kamar takuba
su harba kalmominsu kamar kibiyoyi masu kisa.
4 Sukan yin kwanto su harbi marar laifi;
sukan yi harbi nan da nan, ba tsoro.
5 Sukan ƙarfafa juna a mugayen ƙulle-ƙullensu,
sukan yi magana yadda za su ɓoye tarkunansu;
su ce, “Wa zai gan su?”*Ko kuwa mu
6 Sukan yi ƙulle-ƙullen rashin adalci su ce,
“Mun gama ƙulla cikakkiyar maƙarƙashiya tsab!”
Zuciyar mutum da tunaninsa, suna da wuyar ganewa.
7 Amma Allah zai harbe su da kibiyoyi;
nan da nan za a buge su su fāɗi.
8 Zai juya harshensu a kansu
yă kuma kawo su ga hallaka;
duk waɗanda suka gan su za su kaɗa kai, suna musu ba’a.
9 Dukan mutane za su ji tsoro;
za su yi shelar ayyukan Allah
su kuma yi tunanin abin da ya aikata.
10 Bari masu adalci su yi farin ciki a cikin Ubangiji
su kuma nemi mafaka a gare shi;
bari dukan masu gaskiya a zuciya su yabe shi!