Zabura 69
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin.” Ta Dawuda.
1 Ka cece ni, ya Allah,
gama ruwa ya kai wuyata
2 Na nutse cikin laka mai zurfi,
inda babu wurin tsayawa.
Na shiga cikin ruwaye masu zurfi;
rigyawa ya sha kaina.
3 Na gaji da kira ina neman taimako;
maƙogwarona ya bushe
idanuna sun dushe,
suna neman Allahna.
4 Waɗanda suke ƙina ba dalili
sun fi gashin kaina yawa;
da yawa ne abokan gābana babu dalili,
su da suke nema su hallaka ni.
An tilasta mini in
mayar da abin da ban sata ba.
5 Ka san wautata, ya Allah;
laifina ba a ɓoye yake daga gare ka ba.
6 Bari waɗanda suke sa zuciya gare ka
kada su sha kunya saboda ni,
Ya Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki;
bari waɗanda suke neman ka
kada su sha kunya saboda ni,
Ya Allah na Isra’ila.
7 Gama na jimre da ba’a saboda kai,
kunya kuma ta rufe fuskata.
8 Ni baƙo ne a cikin ’yan’uwana,
bare kuma ga ’ya’yan mahaifiyata maza;
9 gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata,
kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina.
10 Sa’ad da na yi kuka na kuma yi azumi
dole in jimre da ba’a;
11 sa’ad da na sanya rigunan makoki,
mutane suna maishe ni abin dariya.
12 Masu zama a ƙofa suna mini ba’a,
na zama waƙa a bakin bugaggu da giya.
13 Amma na yi addu’a gare ka, ya Ubangiji,
a lokacin da ka ga dama;
a cikin ƙaunarka mai girma, ya Allah,
ka amsa mini da tabbacin ceto.
14 Ka fid da ni daga laka,
kada ka bari in nutse;
ka cece ni daga waɗanda suke ƙina,
daga rurin ruwaye.
15 Kada ka bar rigyawa yă sha kaina
ko zurfafa su haɗiye ni
ko rami yă rufe bakinsa a kaina.
16 Ka amsa mini, ya Ubangiji cikin alherin ƙaunarka;
cikin jinƙanka mai girma ka juyo gare ni.
17 Kada ka ɓoye fuskarka daga bawanka;
ka amsa mini da sauri, gama ina cikin wahala.
18 Ka zo kusa ka kuɓutar da ni;
ka fanshe ni saboda maƙiyana.
19 Ka san yadda ake mini ba’a, ake kunyatar da ni da kuma yadda nake shan kunya;
dukan abokan gābana suna a gabanka.
20 Ba’a ta sa zuciyata ta karai
ta bar ni ba mataimaki;
Na nemi a ji tausayina, amma ban sami ko ɗaya ba,
na nemi masu ta’aziyya, amma ban sami ko ɗaya ba.
21 Sun sa abin ɗaci cikin abincina
suka kuma ba ni ruwan inabi mai tsami sa’ad da nake jin ƙishi.
22 Bari teburin da aka shirya a gabansu yă zama musu tarko;
bari yă zama sakamakon laifi da kuma*Ko kuwa tarko / zumuncinsu kuma yă zama tarko.
23 Bari idanunsu yă dushe don kada su gani,
bayansu kuma yă tanƙware har abada.
24 Ka kwarara fushinka a kansu;
bari fushinka mai zafi yă ci musu.
25 Bari wurinsu yă zama kufai;
kada ka bar wani yă zauna a tentunansu.
26 Gama sun tsananta wa waɗanda ka hukunta
suna kuma taɗin wahalar waɗanda ka ji musu rauni.
27 Ka neme su da laifi a kan laifi;
kada ka bar su su sami rabo a cikin cetonka.
28 Bari a shafe su sarai daga littafin rai
kada a kuma lissafta su tare da adalai.
29 Ina cikin zafi da kuma azaba;
bari cetonka, ya Allah, yă tsare ni.
30 Zan yabe sunan Allah cikin waƙa
in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.
31 Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya,
fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa.
32 Matalauta za su gani su kuma yi murna,
ku da kuke neman Allah, bari zukatanku su rayu!
33 Ubangiji yakan ji masu bukata
ba ya kuwa ƙyale kamammun mutanensa.
34 Bari sama da ƙasa su yabe shi,
tekuna da dukan abin da yake motsi a cikinsu,
35 gama Allah zai cece Sihiyona
yă sāke gina biranen Yahuda.
Sa’an nan mutane za su zauna a can su mallake ta,
36 ’ya’yan bayinsa za su gāje ta,
waɗanda kuma suna ƙaunar sunansa za su zauna a can.