Zabura 85
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce.
Ka nuna wa ƙasarka alheri, ya Ubangiji;
ka mai da nasarorin Yaƙub.
Ka gafarta laifin mutanenka
ka kuma shafe dukan zunubansu.
Sela
Ka kau da dukan fushinka
ka kuma juye daga hasalar fushinka.
 
Ka sāke mai da mu, ya Allah Mai Cetonmu,
ka kau da rashin jin daɗinka daga gare mu.
Za ka ci gaba da fushi da mu har abada ne?
Za ka ja fushinka cikin dukan tsararraki?
Ba za ka sāke raya mu ba,
don mutanenka su yi farin ciki a cikinka?
Ka nuna mana ƙaunarka marar ƙarewa, ya Ubangiji,
ka kuma ba mu cetonka.
 
Zan saurari abin da Allah Ubangiji zai faɗa;
ya yi alkawarin salama ga mutanensa, tsarkakansa,
amma kada su koma ga wauta.
Tabbatacce cetonsa yana kusa da waɗanda suke tsoronsa,
don ɗaukakarsa ta zauna a cikin ƙasarmu.
 
10 Ƙauna da aminci za su sadu;
adalci da salama za su yi wa juna sumba.
11 Aminci zai ɓulɓulo daga ƙasa,
adalci kuma yă duba daga sama.
12 Ubangiji tabbatacce zai bayar da abin da yake da kyau,
ƙasarmu kuwa za tă ba da amfaninta.
13 Adalci na tafiya a gabansa
yana shirya hanya domin ƙafafunsa.