Zabura 92
Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci.
1 Yana da kyau a yabi Ubangiji
a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,
2 don a yi shelar ƙaunarka da safe
amincinka kuma da dare,
3 da kiɗin molo mai tsirkiya goma
da kuma ƙarar garaya.
4 Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji;
na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka.
5 Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji,
tunaninka da zurfi suke ƙwarai!
6 Mutum marar azanci ba zai sani ba,
wawa ba zai gane ba,
7 cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa
kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka,
za a hallaka su har abada.
8 Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada.
9 Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji,
tabbatacce abokan gābanka za su hallaka;
za a watsar da dukan masu aikata mugunta.
10 Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna;
an zubo mai masu kyau a kaina.
11 Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana;
kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana.
12 Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino,
za su yi girma kama al’ul na Lebanon;
13 da aka daddasa a gidan Ubangiji,
za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu.
14 Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu,
za su kasance ɗanye kuma kore shar,
15 suna shela cewa, “Ubangiji adali ne;
shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”