Zabura 98
Zabura ce.
1 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,
gama ya yi abubuwa masu banmamaki;
hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki
sun yi masa aikin ceto.
2 Ubangiji ya sanar da cetonsa
ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai.
3 Ya tuna da ƙaunarsa
da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila;
dukan iyakar duniya sun ga
ceton Allahnmu.
4 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya,
ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;
5 ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya,
da garaya da ƙarar rerawa,
6 tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago,
ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki.
7 Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa,
duniya da kuma kome da yake cikinta.
8 Bari koguna su tafa hannuwansu,
bari duwatsu su rera tare don farin ciki;
9 bari su rera a gaban Ubangiji,
gama yana zuwa domin yă hukunta duniya.
Zai hukunta duniya da adalci
mutane kuma cikin gaskiya.