Zabura 112
Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji,
wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa.
2 ’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar;
tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka.
3 Wadata da arziki suna a cikin gidansa,
adalcinsa zai dawwama har abada.
4 Ko a cikin duhu haske kan haskaka wa mai aikata gaskiya,
mai alheri mai tausayi da kuma mai adalci.‡Ko kuwa / gama Ubangiji mai alheri ne, mai tausayi da kuma mai adalci.
5 Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake,
shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya.
6 Tabbatacce ba zai taɓa jijjigu ba;
za a tuna da mai adalci har abada.
7 Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba;
zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji.
8 Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba;
a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa.
9 Ya rarraba kyautansa ga matalauta,
adalcinsa zai dawwama har abada;
za a ɗaga ƙahonsa§Ƙaho a nan yana nufin girma. sama da bangirma.
10 Mugun mutum zai gani yă kuma yi fushi,
zai ciza haƙora yă kuma lalace;
sha’awace-sha’awacen mugaye za su zo ga ƙarshe.
*^ Wannan Zabura waƙa ce, layinta sun fara da jerin harufan Ibraniyanci bi da bi.
†Zabura 112:1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya
‡Zabura 112:4 Ko kuwa / gama Ubangiji mai alheri ne, mai tausayi da kuma mai adalci.
§Zabura 112:9 Ƙaho a nan yana nufin girma.