*Wannan Zabura waƙa ce, ayoyin kowane layi sun fara da irin harufan ɗaya na Ibraniyanci.
Zabura 119
א Alef
Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi,
waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji.
Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa
suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu.
Ba sa yin wani abin da ba daidai ba;
suna tafiya a hanyoyinsa.
Ka shimfiɗa farillan
da dole a yi biyayya da su.
Kash, da a ce hanyoyina tsayayyu ne
a yin biyayya da ƙa’idodinka mana!
Da ba zan sha kunya ba
sa’ad da na lura da dukan umarnanka.
Zan yabe ka da zuciya ta gaskiya
yayinda nake koyon dokokinka masu adalci.
Zan yi biyayya da ƙa’idodinka;
kada ka yashe ni ɗungum.
ב Bet
Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta?
Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka.
10 Na neme ka da dukan zuciyata;
kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.
11 Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata
don kada in yi maka zunubi.
12 Yabo ya tabbata gare ka, ya Ubangiji;
ka koya mini ƙa’idodinka.
13 Da leɓunana na ba da labarin
dukan dokokin da suka fito bakinka.
14 Na yi farin ciki da bin farillanka
yadda mutum yakan yi farin ciki da arziki mai yawa.
15 Na yi tunani a kan farillanka
na kuma lura da hanyoyinka.
16 Na yi murna a cikin ƙa’idodinka;
ba zan ƙyale maganarka ba.
ג Gimel
17 Ka yi alheri ga bawanka, zan kuwa rayu;
zan yi biyayya da maganarka.
18 Ka buɗe idanuna don in iya gani
abubuwan banmamaki a cikin dokarka.
19 Ni baƙo ne a duniya;
kada ka ɓoye mini umarnanka.
20 Zuciyata ta ƙosa saboda marmari
don dokokinka koyaushe.
21 Ka tsawata wa masu fariya, waɗanda suke la’anta
waɗanda kuma suka kauce daga umarnanka.
22 Ka cire mini ba’a da reni,
gama ina kiyaye farillanka.
23 Ko da yake masu mulki sun zauna tare suna ɓata mini suna,
bawanka zai yi tunani a kan ƙa’idodinka.
24 Farillanka ne abin farin cikina;
su ne mashawartana.
ד Dalet
25 An kwantar da ni ƙasa cikin ƙura;
ka kiyaye raina bisa ga maganarka.
26 Na ba da labari hanyoyina ka kuma amsa mini;
ka koya mini ƙa’idodinka.
27 Bari in gane koyarwar farillanka;
sa’an nan zan yi tunani a kan abubuwan banmamakinka.
28 Raina ya gaji da baƙin ciki;
ka ƙarfafa ni bisa ga maganarka.
29 Ka kiyaye ni daga hanyoyin ruɗu;
ka yi mini alheri ta wurin dokokinka.
30 Na zaɓi hanyar gaskiya;
na sa zuciyata a kan dokokinka.
31 Na riƙe farillanka kankan, ya Ubangiji;
kada ka sa in sha kunya.
32 Ina gudu a kan hanyar umarnanka,
gama ka ’yantar da zuciyata.
ה He
33 Ka koya mini Ya Ubangiji, don in bi ƙa’idodinka;
sa’an nan zan kiyaye su har ƙarshe.
34 Ka ba ni ganewa, zan kuwa kiyaye dokarka
in kuma yi biyayya da ita da dukan zuciyata.
35 Ka bi da ni a hanyar umarnanka,
gama a can zan sami farin ciki.
36 Ka juye zuciyata wajen farillanka
ba wajen riba ta sonkai ba.
37 Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani;
ka kiyaye raina bisa ga maganarka.
38 Ka cika alkawarinka ga bawanka,
saboda a ji tsoronka.
39 Ka kawar da shan kunyar da nake tsoro,
gama dokokinka nagari ne.
40 Ina marmarin farillanka ƙwarai!
Ka kiyaye raina cikin adalcinka.
ו Waw
41 Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zo gare ni, ya Ubangiji,
cetonka bisa ga alkawarinka;
42 sa’an nan zan amsa wa masu cin mutuncina,
gama na dogara ga maganarka.
43 Kada ka ƙwace maganarka daga bakina,
gama na sa zuciyata a dokokinka.
44 Kullayaumi zan yi biyayya da dokokinka,
har abada abadin.
45 Zan yi ta yawo a sake
gama na nemi farillanka.
46 Zan yi maganar farillanka a gaban sarakuna
ba kuwa za a kunyata ni ba,
47 gama ina farin ciki da umarnanka
saboda ina ƙaunarsu.
48 Na ɗaga hannuwana ga umarnanka, waɗanda nake ƙauna,
ina kuma tunani a kan ƙa’idodinka.
ז Zayin
49 Tuna da maganarka ga bawanka,
gama ka ba ni bege.
50 Ta’aziyyata cikin wahalata ita ce
alkawarinka yana kiyaye raina.
51 Masu fariya suna yi mini ba’a ba tare da an hana su ba,
amma ban rabu da dokar ba.
52 Na tuna da dokokinka na tun dā, ya Ubangiji,
na kuwa sami ta’aziyya a cikinsu.
53 Fushi ya kama ni saboda mugaye,
waɗanda suka keta dokokinka.
54 Ƙa’idodinka su ne kan waƙata
a duk inda na sauka.
55 Da dare na tuna da sunanka, ya Ubangiji,
zan kuwa kiyaye dokarka.
56 Wannan shi ne na saba yi,
ina yin biyayya da farillanka.
ח Het
57 Kai ne rabona, ya Ubangiji;
na yi alkawarin in kiyaye maganarka.
58 Na nemi fuskarka da dukan zuciyata;
ka yi mini alheri bisa ga alkawarinka.
59 Na lura da hanyoyina
na kuma mayar da matakaina ga farillanka.
60 Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba
in yi biyayya da umarnanka.
61 Ko da yake mugaye sun ɗaura ni da igiyoyi,
ba zan manta da dokokinka ba.
62 Da tsakar dare nakan tashi in gode maka
saboda dokokinka masu adalci.
63 Ni aboki ne ga duk mai tsoronka,
ga duk wanda yake bin farillanka.
64 Duniya ta cika da ƙaunarka, ya Ubangiji;
ka koya mini ƙa’idodinka.
ט Tet
65 Ka yi wa bawanka alheri
bisa ga maganarka, ya Ubangiji.
66 Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau,
gama na gaskata a umarnanka.
67 Kafin in sha wahala na kauce,
amma yanzu ina biyayya da maganarka.
68 Kai nagari ne, kuma abin da kake yi yana da kyau;
ka koya mini ƙa’idodinka.
69 Ko da yake masu fariya sun shafe ni da ƙarairayi,
na kiyaye farillanka da dukan zuciyata.
70 Zukatansu sun yi tauri da kuma marasa tausayi
amma ina farin ciki a dokarka.
71 Ya yi kyau da na sha wahala
don in koyi ƙa’idodinka.
72 Doka daga bakinka ya fi mini daraja
fiye da azurfa da zinariya guda dubu.
י Yod
73 Hannuwanka ne suka yi suka kuma siffanta ni;
ka ba ni ganewa don in koyi umarnanka.
74 Bari waɗanda suke tsoronka su yi farin ciki sa’ad da suke gan ni,
gama na sa zuciyata a maganarka.
75 Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne,
kuma cikin aminci ka hore ni.
76 Bari ƙaunarka marar ƙarewa tă yi mini ta’aziyya,
bisa ga alkawarinka ga bawanka.
77 Bari tausayinka yă zo mini don in rayu,
gama dokarka ce farin cikina.
78 Bari masu girman kai su sha kunya saboda abubuwa marasa kyau da suke yi mini ba dalili;
amma zan yi tunani a kan farillanka.
79 Bari waɗanda suke tsoronka su juya gare ni,
waɗanda suka gane da farillanka.
80 Bari zuciyata ta kasance marar abin zargi wajen ƙa’idodinka,
don kada in sha kunya.
כ Kaf
81 Raina ya tafke da marmari don cetonka,
amma na sa zuciyata a maganarka.
82 Idanuna sun gaji, suna jiran alkawarinka;
Na ce, “Yaushe za ka ta’azantar da ni?”
83 Ko da yake ni kamar salkar ruwan inabi ne a cikin hayaƙi,
ban manta da ƙa’idodinka ba.
84 Har yaushe bawanka zai yi ta jira?
Yaushe za ka hukunta masu tsananta mini?
85 Masu girman kai sun haƙa mini rami,
sun ƙetare dokarka.
86 Dukan umarnanka abin dogara ne;
ka taimake ni, gama mutane suna tsananta mini ba dalili.
87 Sun kusa gama da ni a duniya,
amma ban bar bin farillanka ba.
88 Ka kiyaye raina bisa ga ƙaunarka,
zan kuwa yi biyayya da farillan bakinka.
ל Lamed
89 Maganarka, ya Ubangiji madawwamiya ce;
tana nan daram a cikin sammai.
90 Amincinka yana cin gaba cikin dukan zamanai;
ka kafa duniya ta kuma dawwama.
91 Dokokinka sun dawwama har yă zuwa yau,
gama dukan abubuwa suna maka hidima.
92 Da ba don dokarka ce farin cikina ba,
da na hallaka a cikin azabana.
93 Ba zan taɓa manta da farillanka ba,
gama ta wurinsu ne ka kiyaye raina.
94 Ka cece ni, gama ni naka ne;
na yi ƙoƙarin neman farillanka.
95 Mugaye suna jira su hallaka ni,
amma zan yi ta tunani a kan farillanka.
96 Ga duk cikakke na ga kāsawa;
amma umarnanka ba su da iyaka.
מ Mem
97 Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka!
Ina tunani a kanta dukan yini.
98 Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana,
gama kullum suna tare da ni.
99 Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina,
gama ina tunani a kan farillanka.
100 Ina da ganewa fiye da dattawa,
gama ina biyayya da farillanka.
101 Na kiyaye ƙafafuna daga kowace muguwar hanya
domin in yi biyayya da maganarka.
102 Ban rabu da dokokinka ba,
gama kai da kanka ne ka koya mini.
103 Ɗanɗanon maganarka akwai zaki,
sun ma fi zuma zaki a bakina!
104 Na sami ganewa daga farillanka;
saboda haka ina ƙin kowace hanyar da ba daidai ba.
נ Nun
105 Maganarka fitila ce ga ƙafafuna
haske kuma a kan hanyata.
106 Na yi rantsuwa na kuma tabbatar da shi,
cewa zan bi dokokinka masu adalci.
107 Na sha wahala sosai;
ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga maganarka.
108 Ka karɓi yabon bakina da nake yi da yardar rai, ya Ubangiji,
ka kuwa koya mini dokokinka.
109 Ko da yake kullum ina riƙe da raina a hannuwana,
ba zan manta da dokarka ba.
110 Mugaye sun kafa mini tarko,
amma ban kauce daga farillanka ba.
111 Farillanka su ne gādona har abada;
su ne farin cikin zuciyata.
112 Zuciyata ta shirya a kan kiyaye ƙa’idodinka
har ƙarshe.
ס Samek
113 Na ƙi mutane masu baki biyu,
amma ina ƙauna dokarka.
114 Kai ne mafakata da garkuwata;
na sa zuciyata a maganarka.
115 Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta,
don in kiyaye umarnan Allahna!
116 Ka raya ni bisa ga alkawarinka, zan kuwa rayu;
kada ka bari a gwale sa zuciyata.
117 Ka riƙe ni za a kuma cece ni;
kullayaumi zan ɗauka ƙa’idodinka da muhimmanci.
118 Ka ki dukan waɗanda suka kauce daga ƙa’idodinka,
gama yaudararsu banza ne.
119 Dukan mugayen duniya ka zubar kamar datti;
saboda haka nake ƙaunar farillanka.
120 Naman jikina na rawan jiki don tsoronka;
na cika da tsoron dokokinka.
ע Ayin
121 Na aikata abin da yake mai adalci da kuma daidai;
kada ka ni a hannun masu danne ni.
122 Ka tabbatar da lafiyar bawanka;
kada ka bar masu girman kai su danne ni.
123 Idanuna sun gaji, da jiran cetonka,
da jiran alkawarinka mai adalci.
124 Ka yi da bawanka bisa ga ƙaunarka
ka kuma koya mini ƙa’idodinka.
125 Ni bawanka ne, ka ba ni fahimi
don in gane farillanka.
126 Lokaci ya yi da za ka yi wani abu, ya Ubangiji;
ana karya dokarka.
127 Saboda ina ƙaunar umarnanka
fiye da zinariya, kai, fiye da zinariya zalla,
128 saboda kuma ina lura da dukan farillanka da kyau,
na ƙi kowace hanyar da ba daidai ba.
פ Fe
129 Farillanka masu banmamaki ne;
saboda haka nake yin biyayya da su.
130 Fassarar maganganunka sukan ba da haske;
sukan ba da ganewa ga marar ilimi.
131 Ina hakkin da bakina a buɗe,
ina marmarin umarnanka.
132 Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai,
yadda kullum ka yi wa waɗanda suke ƙaunar sunanka.
133 Ka bi da sawuna bisa ga maganarka;
kada ka bar zunubi yă mallake ni.
134 Ka fanshe ni daga mutane masu danniya,
don in yi biyayya da farillanka.
135 Ka sa fuskarka ta haskaka a kan bawanka
ka kuma koya mini ƙa’idodinka.
136 Hawaye suna malalowa daga idanuna kamar rafi,
gama ba a biyayya da dokarka.
צ Tsade
137 Mai adalci ne kai, ya Ubangiji,
dokokinka kuma daidai ne.
138 Farillan da ka shimfiɗa masu adalci ne;
su kuma abin dogara ne ƙwarai.
139 Kishina ya cinye ni ɗungum,
gama abokan gābana sun yi biris da maganganunka.
140 An gwada alkawuranka sarai,
bawanka kuwa yana ƙaunarsu.
141 Ko da yake ni ba kome ba ne an kuwa rena ni,
ba na manta da farillanka.
142 Adalcinka dawwammame ne
dokar kuma gaskiya ce.
143 Wahala da damuwa suna a kaina,
amma umarnanka su ne farin cikina.
144 Farillanka daidai ne har abada;
ka ba ni ganewa don in rayu.
ק Kof
145 Na yi kira da dukan zuciyata; ka amsa mini, ya Ubangiji,
zan kuwa yi biyayya da ƙa’idodinka.
146 Na yi kira gare ka; ka cece ni
zan kuwa kiyaye farillanka.
147 Na tashi kafin fitowar rana na kuma yi kukan neman taimako;
na sa zuciyata a maganarka.
148 Ban rufe idanuna ba dukan dare,
don in yi tunani a kan alkawuranka.
149 Ka ji muryata bisa ga ƙaunarka;
ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga dokokinka.
150 Waɗanda suke ƙirƙiro mugayen dabaru suna nan kusa,
amma suna nesa da dokarka.
151 Duk da haka kana kusa, ya Ubangiji,
kuma dukan umarnanka gaskiya ne.
152 Tun tuni na koyi daga farillanka
cewa ka kafa su su kasance har abada.
ר Resh
153 Ka dubi wahalata ka cece ni,
gama ban manta da dokarka ba.
154 Ka kāre manufata ka kuma fanshe ni,
ka cece rai na kamar yadda ka alkawarta!
155 Ceto yana nesa da mugaye,
gama ba sa neman ƙa’idodinka.
156 Tausayinka da girma yake, ya Ubangiji;
ka kiyaye raina bisa ga dokokinka.
157 Maƙiya masu yawa ne suke tsananta mini,
amma ban rabu da farillanka ba.
158 Na dubi marasa aminci da ƙyama,
gama ba sa yin biyayya da maganarka.
159 Dubi yadda nake ƙaunar farillanka;
ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga ƙaunarka.
160 Dukan maganganunka gaskiya ne;
dukan dokokinka masu adalci madawwami ne.
ש Sin da Shin
161 Masu mulki suna tsananta mini ba dalili,
amma zuciyata na rawan jiki game da maganarka.
162 Ina farin ciki da alkawarinka
kamar yadda wani kan sami ganima mai girma.
163 Na ƙi ina kuma ƙyamar ƙarya
amma ina ƙaunar dokarka.
164 Sau bakwai a rana ina yabonka
saboda dokokinka masu adalci.
165 Waɗanda suke ƙaunar dokarka suna da babban salama,
kuma babu abin da zai sa su yi tuntuɓe.
166 Ina jiran cetonka, ya Ubangiji,
ina kuma bin umarnanka.
167 Ina biyayya da farillanka,
gama ina ƙaunarsu ƙwarai.
168 Ina biyayya da farillanka da kuma koyarwarka,
gama dukan hanyoyina sanannu ne gare ka.
ת Taw
169 Bari kukata ta zo gare ka, ya Ubangiji;
ka ba ni ganewa bisa ga maganarka.
170 Bari roƙona yă zo gabanka;
ka cece ni bisa ga alkawarinka.
171 Bari leɓunana su cika da yabonka,
gama ka koya mini ƙa’idodinka.
172 Bari harshena yă rera game da maganarka,
gama dukan umarnanka masu adalci ne.
173 Bari hannunka yă kasance a shirye don yă taimake ni,
gama na zaɓi farillanka.
174 Ina marmarin cetonka, ya Ubangiji,
dokarka kuwa ita ce farin cikina.
175 Bari in rayu don in yabe ka,
bari kuma dokokinka su raya ni.
176 Na kauce kamar ɓatacciyar tunkiya.
Ka nemi bawanka,
gama ban manta da umarnanka ba.

*^ Wannan Zabura waƙa ce, ayoyin kowane layi sun fara da irin harufan ɗaya na Ibraniyanci.