Zabura 137
A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kuka
sa’ad da muka tuna da Sihiyona.
A can a kan rassan itatuwa
muka rataye garayunmu,
gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi,
masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki;
suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!”
 
Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangiji
a baƙuwar ƙasa?
In na manta da ke, ya Urushalima,
bari hannuna na dama manta da iyawarsa.
Bari harshena yă manne wa rufin bakina
in ban tuna da ke ba,
in ban so Urushalima
farin cikin mafi girma ba.
 
Ka tuna, ya Ubangiji, abin da mutanen Edom suka yi
a ranar da Urushalima ta fāɗi.
Suka yi ihu suka ce, “A ragargaza ta,
A ragargaza ta har tushenta!”
Ya Diyar Babilon, an ƙaddara ke zuwa hallaka,
mai farin ciki ne wanda ya sāka miki
saboda abin da kika yi mana,
shi da ya ƙwace jariranki
ya fyaɗa su a kan duwatsu.