Zabura 140
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
1 Ka cece ni, ya Ubangiji, daga mugaye;
ka tsare ni daga mutane masu rikici,
2 masu shirya maƙarƙashiya a zukatansu
suna kuma kawo yaƙi kullum.
3 Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji;
dafin gamsheƙa yana a leɓunansu.
Sela
4 Ka kiyaye ni, ya Ubangiji, daga hannuwan mugaye;
ka tsare ni daga mutane masu rikici
waɗanda suke shirin kwashe ni a ƙafafu.
5 Masu girman kai sun sa mini tarko;
sun shimfiɗa igiyoyin ragarsu
sun kuma shirya mini tarko a hanyata.
Sela
6 Ya Ubangiji, na ce maka, “Kai ne Allahna.”
Ka ji kukata ta neman jinƙai, ya Ubangiji.
7 Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mai fansana mai ƙarfi,
wanda yake garkuwoyin kaina a ranar yaƙi.
8 Kada ka biya wa mugaye bukatunsu, ya Ubangiji;
kada ka bar shirinsu su yi nasara,
in ba haka ba za su yi fariya.
Sela
9 Bari kawunan waɗanda suka kewaye ni
su rufu da masifun da leɓunansu suka jawo.
10 Bari garwashin wuta yă zubo a kansu;
bari a jefar da su cikin wuta,
cikin rami mai zurfi, kada su sāke tashi.
11 Kada masu ɓata suna su taɓa kahu a ƙasar;
bari masifa ta farauci mutane masu rikici.
12 Na san cewa Ubangiji ya shirya wa matalauta adalci
yana kuma yi wa mabukata adalci.
13 Tabbatacce masu adalci za su yabi sunanka
masu aikata gaskiya kuma za su zauna a gabanka.