*Wannan Zabura waƙa ce, ayoyin waɗanda suka (haɗa da aya 13b) sun fara da irin harufa ɗaya bayan ɗaya na Ibraniyanci.
Zabura 145
Zabura ce ta yabo. Ta Dawuda.
Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki;
zan yabi sunanka har abada abadin.
Kowace rana zan yabe ka
in kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin.
 
Ubangiji da girma yake ya kuma cancanci yabo
girmansa ya fi ƙarfin ganewar mutum.
Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara;
za su yi magana game da manyan ayyukanka.
Za su yi zancen ɗaukakarka mai daraja,
zan kuma yi tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.
Za su yi magana game da ikon ayyukanka masu bantsoro,
zan kuma yi shelar manyan ayyukanka.
Za su yi bikin yalwar alherinka
suka kuma rera adalcinka da farin ciki.
 
Ubangiji mai alheri da kuma tausayi,
mai jinkirin fushi cike kuma da ƙauna.
 
Ubangiji nagari ne ga duka;
yana tausayin dukan abubuwan da ya yi.
10 Dukan abubuwan da ka yi za su yabe ka, ya Ubangiji;
tsarkakanka za su ɗaukaka ka.
11 Za su yi maganar ɗaukakar mulkinka
za su kuma yi zancen ikonka,
12 saboda dukan mutane su san manyan ayyukanka
da ɗaukakar darajar mulkinka.
13 Mulkinka madawwamin mulki ne,
sarautarka kuma za tă dawwama cikin dukan zamanai.
 
Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransa
mai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi.
14 Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗi
yana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa.
15 Idanun kowa yana dogara gare ka,
kana kuma ba su abincinsu a lokacin da ya dace.
16 Ka buɗe hannunka
ka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai.
 
17 Ubangiji mai adalci ne cikin dukan hanyoyinsa
yana kuma nuna ƙauna ga dukan abubuwan da ya yi.
18 Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi,
ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.
19 Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa;
yakan ji kukansu yă kuma cece su.
20 Ubangiji yakan lura da dukan waɗanda suke ƙaunarsa,
amma dukan mugaye zai hallaka su.
 
21 Bakina zai yi magana cikin yabon Ubangiji.
Bari kowace halitta ta yabi sunansa mai tsarki
har abada abadin.

*^ Wannan Zabura waƙa ce, ayoyin waɗanda suka (haɗa da aya 13b) sun fara da irin harufa ɗaya bayan ɗaya na Ibraniyanci.