10
’Yan’uwa, abin da zuciyata take so da kuma addu’ata ga Allah saboda Isra’ilawa shi ne su sami ceto. Gama na shaida su a kan suna da kishi bin Allah, sai dai kishinsu ba a bisa sani ba. Da yake ba su san adalcin da yake fitowa daga Allah ba suka kuma nemi su kafa nasu, sai suka ƙi miƙa kai ga adalcin Allah. Kiristi shi ne ƙarshen doka domin a sami adalci wa kowane mai bangaskiya.
Musa ya bayyana adalcin da yake ga Doka cewa, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”*Fir 18.5 Amma adalcin da yake ga bangaskiya yana cewa, “Kada ka faɗa a zuciyarka, ‘Wa zai hau sama?’ ”M Sh 30.13 (wato, don yă sauko da Kiristi), “ko kuwa ‘Wa zai gangara can zurfin ƙasa?’ ” (wato, don yă hauro da Kiristi daga matattu). Amma mene ne aka ce? “Maganar tana kusa da kai; tana cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka,”M Sh 30.14 wato, maganar bangaskiyan nan da muke shela. Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto. 10 Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka. 11 Kamar yadda Nassi ya ce, “Duk wanda ya gaskata da shi ba zai taɓa shan kunya ba.”§Ish 28.16 12 Gama ba bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa yana kuma ba da albarka a yalwace ga duk masu kira gare shi, 13 gama, “Duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.”*Yow 2.32
14 To, ta yaya za su kira ga wanda ba su gaskata ba? Ta yaya kuma za su gaskata wanda ba su taɓa ji ba? Ta yaya kuma za su ji ba tare da wani ya yi musu wa’azi ba? 15 Kuma ta yaya za su yi wa’azi in ba an aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Isowar masu kawo labari mai daɗi abu mai kyau ne ƙwarai!”Ish 52.7
16 Amma ba dukan Isra’ilawa ne suka karɓi labari mai daɗin nan ba. Gama Ishaya ya ce, “Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu?”Ish 53.1 17 Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi. 18 Amma ina tambaya, “Ba su ji ba ne? Tabbatacce sun ji.
“Muryarsu ta tafi ko’ina a cikin duniya,
kalmominsu kuma har iyakar duniya.ӤZab 19.4
19 Har wa yau, ina da tambaya. Shin, Isra’ila ba su fahimta ba ne? Da farko, Musa ya ce,
“Zan sa ku yi kishin waɗanda ba al’umma ba;
zan sa ku yi fushin al’ummar da ba ta da fahimta.”*M Sh 32.21
20 Ishaya kuma ya fito gabagadi ya ce,
“Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni;
Na bayyana kaina ga waɗanda ba su ma taɓa neman sanina ba.”
21 Amma game da Isra’ila ya ce,
“Dukan yini na miƙa hannuwana
ga mutane marasa biyayya da masu taurinkai.”Ish 65.2

*10:5 Fir 18.5

10:6 M Sh 30.13

10:8 M Sh 30.14

§10:11 Ish 28.16

*10:13 Yow 2.32

10:15 Ish 52.7

10:16 Ish 53.1

§10:18 Zab 19.4

*10:19 M Sh 32.21

10:21 Ish 65.2