2
Ƙaunatacciya*Ko kuma Ƙaunatacce
1 Ni furen bi-rana ne na Sharon,
furen bi-rana na kwari.
Ƙaunatacce
2 Kamar furen bi-rana a cikin ƙayayyuwa
haka ƙaunatacciyata take a cikin ’yan mata.
Ƙaunatacciya
3 Kamar itacen gawasa a cikin itatuwan jeji
haka ƙaunataccena yake a cikin samari.
Ina farin ciki in zauna a inuwarsa,
’ya’yan itacensa suna da daɗin ɗanɗanon da nake so
4 Ya kai ni babban zauren da ake liyafa,
ƙauna ita ce tutarsa a gare ni.
5 Ka ƙarfafa ni da zabibi
ka wartsake ni da gawasa,
gama ina suma don ƙauna.
6 Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina,
hannunsa na dama kuma ya rungume ni.
7 ’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari
da bareyi da ƙishimai na jeji.
Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba
sai haka ya zama lalle.
8 Saurara! Ƙaunataccena!
Duba! Ga shi ya iso,
yana tsalle a duwatsu,
yana rawa a bisa tuddai.
9 Ƙaunataccena yana kama da barewa ko sagarin ƙishimi
Duba! Ga shi can tsaye a bayan katangarmu,
yana leƙe ta tagogi,
yana kallo ta cikin asabari.
10 Ƙaunataccena ya yi magana ya ce mini,
“Tashi, ƙaunatacciyata,
kyakkyawata, ki zo tare da ni.
11 Duba! Damina ta wuce;
ruwan sama ya ɗauke ya kuma ƙare.
12 Furanni sun hudo a duniya;
lokaci yin waƙa ya zo,
ana jin kukan kurciyoyi
ko’ina a ƙasarmu.
13 Itacen ɓaure ya fid da ’ya’yansa da sauri;
tohon inabi suna ba da ƙanshinsu.
Tashi, zo, ƙaunatacciyata;
kyakkyawata, zo tare da ni.”
Ƙaunataccena
14 Kurciyata a kogon dutse,
a wuraren ɓuya a gefen dutse,
nuna mini fuskarki,
bari in ji muryarki;
gama muryarki da daɗi take,
fuskarki kuma kyakkyawa ce.
15 Kama mana ɓeraye,
ƙananan ɓerayen
da suke lalatar da gonakin inabi,
gonakin inabinmu da suke cikin yin fure.
Ƙaunatacciya
16 Ƙaunataccena nawa ne ni kuma tasa ce;
yana kiwon garkensa a cikin furannin bi-rana.
17 Sai gari ya waye
inuwa kuma ta watse,
ka juye, ƙaunataccena,
ka zama kamar barewa
ko kamar sagarin ƙishimi
a kan tuddai masu ciyawa.