8
Da a ce kai ɗan’uwa ne gare ni,
wanda nonon mahaifiyata sun shayar!
Da in na same ka a waje,
na sumbace ka,
babu wanda zai rena ni.
Da sai in bi da kai
in kawo ka gidan mahaifiyata,
ita da ta koyar da ni.
Da na ba ka ruwan inabi gaurayayye da kayan yaji ka sha,
zaƙin rumman nawa.
Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina,
hannunsa na dama kuma ya rungume ni.
’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari.
Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba
sai haka ya zama lalle.
Ƙawaye
Wace ce wannan da take haurawa daga hamada
tana dogara a kan ƙaunataccenta?
Ƙaunatacciya
A ƙarƙashin itacen gawasa na farkar da ke,
a wurin da aka haife ki,
wurin da mahaifiyarki ta haife ki.
Ka sa ni kamar hatimi a zuciyarka,
kamar hatimi a hannunka;
gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa,
kishinta yana kamar muguntar kabari,
yana ƙuna kamar wuta mai ci,
kamar gagarumar wuta.*Ko kuwa / kamar harshen wutar Ubangiji.
Ruwa da yawa ba zai iya kashe ƙauna ba,
koguna ba za su iya kwashe ta ba.
In wani zai bayar da
dukan dukiyar gidansa don ƙauna,
za a yi masa dariya ne kawai.
Ƙawaye
Muna da ƙanuwa,
nonanta ba su riga sun yi girma ba.
Me za mu yi da ƙanuwarmu
a ranar da za a yi maganar sonta?
Da a ce ita katanga ce,
da sai mu gina hasumiyar azurfa a kanta.
Da a ce ita ƙofa ce,
da sai mun yi mata ƙyauren itacen al’ul.
Ƙaunatacciya
10 Ni katanga ce
kuma nonaina sun yi kamar hasumiya.
Ta haka na zama idanunsa
kamar wanda yake kawo gamsuwa.
11 Solomon ya kasance da gonar inabi a Ba’al-Hamon;
ya ba da hayar gonar inabi ga ’yan haya.
Kowanne zai biya shekel dubu na azurfa
don ’ya’yan inabin.
12 Amma gonar inabina nawa ne da zan bayar;
shekel dubu naka ne, ya Solomon,
kuma ɗari biyu na waɗanda suke lura da ’ya’yan itatuwansa ne.
Ƙaunatacce
13 Ke da kike zaune a cikin lambu
da ƙawaye suna lura da ke,
bari in ji muryarki!
Ƙaunatacciya
14 Ka zo, ƙaunataccena,
ka zama kamar barewa
ko kuwa kamar ’yar batsiya
a kan dutsen da kayan yaji suke a shimfiɗe.

*8:6 Ko kuwa / kamar harshen wutar Ubangiji.