Zakariya
1
Kira don komawa ga Ubangiji
A wata na bakwai na shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.
Ubangiji ya yi fushi sosai da kakanninku. Saboda haka ka gaya wa mutanen, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku komo gare ni,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘ni kuma zan komo gare ku,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na dā suka ce musu, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku juya daga mugayen hanyoyinku da mugayen abubuwan da kuke yi.’ Amma ba su saurara ba, ko ma su kula da ni, in ji Ubangiji. Yanzu ina kakanninku suke? Annabawan kuma fa, sun rayu har abada ne? Amma maganata da dokokina da na umarta ta wurin bayina annabawa fa, ashe, ba su tabbata ba a kan kakanninku?
“Sa’an nan suka tuba suka ce, ‘Ubangiji Maɗaukaki ya yi mana daidai abin da hanyoyinmu suka cancanci mu samu, kamar dai yadda ya yi niyya yi.’ ”
Mutumin a cikin itatuwan ci-zaƙi
7-8 A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato, watan Shebat, a shekara ta biyu ta Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.
Da dare, na ga wahayi, a gabana kuwa ga mutum a kan jan doki! Yana tsaye a cikin itatuwa masu furanni, a bayansa a cikin itatuwan ci-zaƙi, a bayansa kuwa akwai dawakai masu ruwan ja, ruwan ƙasa-ƙasa da kuma ruwan fari.
Sai na yi tambaya na ce, “Mene ne waɗannan ranka yă daɗe?”
Mala’ikan da yake magana da ni ya amsa ya ce, “Zan nuna maka mene ne su.”
10 Sai mutumin da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin ya yi bayani cewa, “Su ne waɗanda Ubangiji ya aika ko’ina a duniya.”
11 Sai suka ce wa mala’ikan da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin, “Mun ratsa ko’ina a duniya, sai muka ga duniya duka tana zaman lafiya.”
12 Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Maɗaukaki, har yaushe za ka ci gaba da ƙi nuna wa Urushalima da kuma garuruwan Yahuda jinƙai, waɗanda kake fushi da su shekarun nan saba’in?” 13 Sai Ubangiji ya yi wa mala’ikan da ya yi magana da ni magana da kalmomi masu daɗi da kuma masu ta’azantarwa.
14 Sai mala’ikan da yake magana da ni ya ce, “Ka yi shelar maganan nan, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ina kishi domin Urushalima da Sihiyona, 15 amma ina fushi da ƙasashen da suke ji suna zaman lafiya, na ɗan yi fushina kawai, amma sai suka ƙara musu masifar.’
16 “Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Zan komo Urushalima da jinƙai, a can ne za a sāke gina gidana. Za a kuma miƙe ma’auni a bisa Urushalima,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
17 “Ci gaba da yin shela, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Garuruwana za su sāke kwarara da wadata, Ubangiji kuma zai sāke yi wa Sihiyona ta’aziyya, yă kuma zaɓi Urushalima.’ ”
Ƙahoni huɗu da maƙera huɗu
18 Sa’an nan na dubi sama a gabana kuwa sai ga ƙahoni huɗu! 19 Na tambayi mala’ikan da yake mini magana, na ce, “Mene ne waɗannan?”
Ya amsa mini ya ce, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda, Isra’ila da kuma Urushalima.”
20 Sa’an nan Ubangiji ya nuna mini maƙera guda huɗu. 21 Na yi tambaya na ce, “Mene ne waɗannan suke zuwa yi?”
Ya amsa ya ce, “Waɗannan ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda har ba wanda yake iya ɗaga kansa, amma maƙeran sun zo don su tsorata su su kuma saukar da ƙahonin ƙasashen nan waɗanda suka ɗaga ƙahoninsu gāba da ƙasar Yahuda don su warwatsa ta.”