4
Wurin ajiye fitilan zinariya da itatuwan zaitun biyu
1 Sai mala’ikan da ya yi magana da ni ya komo ya farkar da ni, kamar yadda ake farkar da mutum daga barcinsa. 2 Ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?”
Na amsa, na ce, “Na ga wurin ajiye fitilan zinariya da kwano a kai, da kuma fitilu bakwai a kansa, da butocin kai wa fitilu mai guda bakwai. 3 Akwai kuma itatuwan zaitun guda biyu a gefensa, ɗaya a gefen dama na kwanon ɗaya kuma a gefen hagunsa.”
4 Na tambayi mala’ikan da ya yi magana da ni na ce, “Mene ne waɗannan, ranka yă daɗe?”
5 Sai ya amsa ya ce, “Ba ka san mene ne waɗannan ba?”
Na amsa, na ce, “A’a, ranka yă daɗe.”
6 Sai ya ce mini, “Wannan ce maganar Ubangiji ga Zerubbabel. ‘Ba ta wurin ƙarfi ba, ko ta wurin iko, sai dai ta wurin Ruhuna,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
7 “Kai mene ne, ya babban dutse? A gaban Zerubbabel za a rushe ka ka zama fili. Sa’an nan Zerubbabel yă kawo dutsen da ya fi kyau, a kuma yi ta sowa ana cewa, ‘Allah yă yi masa albarka! Allah yă yi masa albarka!’ ”
8 Sai maganar Ubangiji ta zo mini, 9 “Hannuwan Zerubbabel sun kafa harsashin haikalin nan; hannuwansa ne kuma za su gama ginin. Sa’an nan ne za ka san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni zuwa wurinka.
10 “Wa ya rena ranar ƙananan abubuwa? Mutane za su yi murna sa’ad da suka ga igiyar gwaji a hannun Zerubbabel.
“Waɗannan guda bakwai ɗin su ne idanun Ubangiji, masu jujjuyawa cikin dukan duniya.”
11 Sai na tambaye shi na ce, “Mene ne waɗannan itatuwan zaitun guda biyu tsaye a hagu da kuma daman wurin ajiye fitilan fitilu?”
12 Na sāke tambaye shi na ce, “Mene ne waɗannan rassa biyun nan na zaitun a gefen bututu biyu na zinariya da suke zuba man zinariya?”
13 Ya amsa ya ce, “Ba ka san mene ne waɗannan ba?”
Na ce, “A’a, ranka yă daɗe.”
14 Sai ya ce, “Waɗannan su ne biyun da aka shafe don*ko kuwa biyun da suke kawo mai su kuma su yi wa Ubangiji dukan duniya hidima.”