Bitrus Ta Fari
1
Bitrus, manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zababbu wadanda suke baki, a warwatse cikin Buntus, Galatiya, kappadokiya, Asiya, da Bitiniya. Bisa ga rigasanin Allah Uba, Ta wurin tsarkakewar Ruhu, zuwa biyayya da yayyafar jinin Yesu Almasihu. Alheri da salama su yawaita a gareku. Albarka ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu. Ta wurin jinkansa mai girma, ya maya haihuwarmu zuwa bege mai rai ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu. Zuwa gado marar lalacewa, marar baci, ba kuma zai kode ba. Wanda aka kebe a sama dominku. Ku da ikon Allah ya kiyaye ta wurin bangaskiya domin ceto wanda za'a bayyana a karshen zamanai. Cikin wannan kuna murna da yawa, duk da ya ke ya zama wajibi gare ku yanzu ku yi bakin ciki, a cikin jarabobi iri iri. Wannan kuwa da nufin a iske aunawar bangaskiyarku ne, bangaskiyar da tafi zinariya daraja, wadda takan lalace ko da an gwada ta da wuta. Wannan ya faru domin bangaskiyan nan taku ta jawo maku yabo da girma da daukaka a bayyanuwar Yesu Almasihu. Wanda kuke kauna, ko da yake baku ganshi ba. Ko da yake baku ganinsa yanzu, duk da haka kun bada gaskiya gare shi murnar da ku ke yi kwarai da farin ciki wanda tafi gaban a fadi cike da daukaka. Kuna karbar sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku. 10 Annabawan da su ka yi annabcin ceton da ya zama naku su ka yi bidassa suka bincike kuma da himma. 11 Sun nemi su san ko wanene da kuma kowanne lokaci ne Ruhun Almasihu da ke cikinsu yake bayyana ma su. Wannan ya faru ne sa'adda yake gaya ma su tun da wuri game da shan wahalar Almasihu da kuma daukakar da zata biyo baya. 12 An kuwa bayyana wa annabawan cewa ba kansu suke hidimtawa ba, amma ku suke yi wa hidima. Wannan shine abin da suke yi game da abin da aka rigaya aka gaya maku, ta wurin wadanda da Ruhu mai Tsarki ya bishe su. Wanda aka aiko daga sama. Wadannan sune abubuwan da mala'iku ma suka yi marmarin a bayyana masu. 13 Domin wannan fa ku natsu. Ku yi dammara a hankalinku. Ku kafa begenku sarai akan alherin da za'a kawo maku a lokacin bayyanuwar Yesu Almasihu. 14 Kamar 'ya'ya masu biyyaya, kada ku biyewa sha'awoyinku na da a zamanin jahilcinku. 15 Amma yadda shi wanda ya kira ku mai tsarki ne, kuma ku zama da tsarki cikin dukkan al'amuranku. 16 Domin a rubuce yake, “Ku zama da tsarki, gama ni mai tsarki ne.” 17 Idan ku na kira bisa gare shi “Uba” shi wanda yake hukuntawa ba da tara ba, amma gwar-gwadon aikin kowane mutum, sai kuyi zaman bakuncinku da tsoro da bangirma. 18 Kun san cewa ba da azurfa ko zinariya mai lalacewa aka fanshe ku ba, daga halinn wauta da kuka gada daga wurin iyayenku. 19 Maimakon haka an fanshe ku da jinin Almasihu mai daraja, marar aibu kamar na dan rago. 20 An zabi Almasihu tun kafin kafawar duniya, amma a karshen zamanu ya bayyanu a gare ku. 21 Ku da kuka bada gaskiya ga Allah ta wurinsa, wanda ya tashe shi daga matattu ya kuma bashi daukaka domin bangaskiyarku da begenku su kasance cikin Allah. 22 Da shike kun tsarkake rayukanku cikin biyayyar ku ga gaskiya zuwa ga sahihiyar kauna ta 'yan'uwa, sai ku kaunaci junanku da zuciya mai gaskiya. 23 da shike an sake hai'huwarku ba daga iri mai lalacewa ba amma daga iri marar rubewa, ta wurin maganar Allah wadda take rayuwa ta kuma dawwama. 24 Gama “dukkan jiki kamar ciyawa yake, dukkan darajarsa kuwa kamar furen ciyawa take. Ciyawa takan yi yaushi, furenta ya kan yankwane ya fadi, 25 amma maganar Ubangiji tabbatacciya ce har abada. “Wannan ita ce maganar bishara wadda akayi maku wa'azinta.”