2 Tasalonikawa
1
Bulus da Silbanus da Timoti, zuwa ga ikilisiyar Tasolonika cikin Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu. Bari alheri ya kasance tare da ku da salama daga Allah Ubanmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu. Lallai ne mu godewa Allah kulluyaumin domin ku, yan'uwa. Domin hakan dai dai ne, saboda bangaskiyarku ta karu sosai, kuma kaunar junanku tana karuwa. Mu da kanmu muna fahariya da ku a ikilisiyoyin Allah. Muna maganar hakurinku da bangaskiyarku a cikin dukkan tsananin da kuke fuskanta. Muna maganar kuncin da kuke jimrewa. Wannan itace alamar shari'ar Allah ta adalci. Sakamakon haka shine za a dauke ku cancantattu na mulkin Allah wanda kuke wahala dominsa. Adalci ne ga Allah ya mayar da kunci ga wadanda suke kuntata maku, ya kuma baku hutu ku dake shan wuya tare da mu. Zai yi haka ne a bayyanar Ubangiji Yesu daga sama da Mala'ikun ikonsa. A cikin wuta mai huruwa zai dau fansa bisa wadanda basu san Allah ba da wadanda basu karbi bisharar Ubangijinmu Yesu almasihu ba. Za su sha azaba ta hallaka har abada daga fuskar Ubangiji da kuma daukakar ikonsa. 10 Zai yi wannan lokacin da yazo a wannan rana don jama'arsa su daukaka shi, kuma ya zama abin mamaki ga dukkan wadanda suka bada gaskiya. Domin kun gaskata shaidarmu a gare ku. 11 Saboda wannan muke addu'a kullum domin ku. Muna addu'a domin Allahnmu ya sa ku cancanci kiran ku. Muna addu'a ya biya ku muradin ku na yin nagarta da dukkan wani aikin bangaskiya da kuma iko. 12 Muna addu'a haka domin sunan Ubangijinmu Yesu ya sami daukaka daga gare ku. Addu'armu itace ya daukaka ku, saboda alherin Allahnmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu.