Yakubu
1
Yakubu, bawan Allah, da kuma Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilun nan goma sha biyu da suke warwatse: ina gaishe ku. Ku dauke su duka da farin ciki, 'yan'uwana, duk sa'adda kuke fuskantar jarabobi. Ku sani cewa gwajin banskiyar ku ta kan haifi jimiri. Bari jimiri ya cika aikin sa, domin ku kai ga cikakken girma kuma ku kammalu, domin kada ku rasa komai. Amma idan waninku yana bukatar hikima, sai ya roki Allah, wanda yake bayarwa a yalwace, ba tare da gori ba ga duk wanda ya roke shi, zai kuwa ba shi. Amma fa sai ya roka da banskiya ba tare da shakka ba, don mai shakka kamar rakumin ruwan teku yake, wanda iska take korarwa tana tunkudawa. Tilas ne wannan mutum kada ya yi tunanin zai karbi wani abu a wurin Ubangiji. Irin wannan mutumin mai zuciya biyu ne, mara tsai da hankali a dukan hanyoyin sa. Bari dan'uwa matalauci ya yi takama da matsayin sa babba, 10 amma mutum mai arziki kuma a kaskantaccen matsayin sa, gama zai shude kamar furen ciyawa na jeji. 11 Domin rana na bullowa da zafi mai konarwa kuma ya busar da ciyawa. Furen ya fadi, kuma kyaun sa ya lalace. Haka ma, mai arziki zai bushe yana cikin tsakiyar tafiyarsa. 12 Albarka ta tabbata ga mutum mai jurewa da gwaji. Domin in ya jure gwajin, zai sami rawanin rai, wanda aka yi alkawarin sa ga wadanda ke kaunar Allah. 13 Kada wani ya ce idan aka gwada shi, ''Wannan gwaji daga wurin Allah ne,'' domin ba a gwada Allah da mugunta, shi kan sa kuwa ba ya gwada kowa. 14 Amma kowanne mutum yakan sami gwaji daga muguwar sha'awar sa, wadda take janye shi kuma ta rinjaye shi. 15 Bayan da muguwar sha'awar ta dauki ciki, sai ta haifi zunubi. Kuma bayan da zunubi ya yi girma, yakan haifi mutuwa. 16 Kada fa ku yaudaru, 'yan'uwana kaunatattu. 17 Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar baiwa daga sama take. Ta sauko ne daga wurin Uban haskoki. Wanda babu sauyawa ko wata alamar sakewa kamar yadda inuwa ke yi. 18 Allah ya zabi ya haife mu ta wurin maganar gaskiya, domin mu zama kamar nunar fari na dukan halittar sa. 19 Kun san wannan, 'yan'uwana kaunatattu: bari kowanne mutum ya yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi. 20 Domin fushin mutum ba ya aikata adalcin Allah. 21 Saboda haka, sai ku yar da kowanne irin aikin kazanta da yalwar mugunta. A cikin tawali'u ku karbi dassashiyar maganar, wadda ke iya ceton rayukan ku. 22 Ku zama masu aikata maganar, kada ku zama masu jin ta kawai, kuna yaudarar kanku. 23 Domin duk wanda ya ke mai jin maganar ne kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutum yake mai duba fuskarsa a madubi. 24 Yakan dubi kansa sai ya tafi, nan da nan kuwa sai ya manta da kamannin sa. 25 Amma duk mai duba shari'ar da bin ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace biyayya da ita, ba zai zama kamar wanda zai ji ya manta ba, wannan mutum zai zama da albarka a cikin abin da yake yi. 26 Idan wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, yana yaudarar zuciyarsa ne, addinin mutumin nan na banza ne. 27 Addini sahihi kuma marar aibi a gaban Allahnmu da Ubanmu, shine a kula da gwauraye da marayu a cikin kuntatar su, kuma mutum ya kebe kansa ya zama marar aibi daga duniya.