7
1 Bayan wadannan abubuwa Yesu ya zagaya cikin Gallili, saboda baya so ya shiga cikin Yahudiya domin Yahudawa suna shirin su kashe shi. 2 To Idin Bukkoki na Yahudawa ya kusa. 3 Sai 'yan'uwansa suka ce da shi, “ka tashi ka tafi Yahudiya, domin almajiranka su ga ayyukan da kake yi su ma. 4 Ba wanda ya ke yin wani abu a boye idan dai yana so kowa da kowa ya san shi. Da yake ka na yin wadannan abubuwa sai ka nuna kan ka a fili ga duniya. 5 Domin ko 'yan'uwansa ma basu bada gaskiya gare shi ba. 6 Yesu ya ce dasu, “lokaci na bai yi ba tukuna, amma ku koyaushe lokacin ku ne. 7 Duniya baza ta iya kin ku ba, amma ta ki ni saboda ina fadin cewa ayyukanta ba su da kyau. 8 Ku ku je wurin idin, ni ba zan je wurin idin ba domin lokacina bai yi ba tukuna. 9 Bayan da ya gaya masu wadannan abubuwa, ya tsaya a cikin Gallili. 10 Amma bayan da 'yan'uwansa su ka tafi wurin idin shi ma ya tafi, amma a asirce ba a fili ba. 11 Saboda Yahudawa suna neman sa a wurin idin, su na cewa “Ina yake?” 12 Akwai maganganu dayawa a kansa cikin taron. Wadansu suna cewa, “shi mutumin kirki ne.” Wadansu kuma suna cewa,”A'a yana karkatar da hankalin jama'a.” 13 Amma duk da haka ba wanda ya yi magana a fili a kansa saboda suna jin tsoron Yahudawa. 14 Sa'anda aka kai rabin idin, sai Yesu ya shiga cikin haikali ya fara koyarwa. 15 Yahudawa suna mamaki suna cewa,”Yaya aka yi wannan mutum ya sami ilimi dayawa haka? Shi kuwa bai je makaranta ba.” 16 Yesu ya ba su amsa ya ce,”Koyarwata ba tawa ba ce, amma ta wanda ya aiko ni ce.” 17 Idan wani yana so ya yi nufinsa, za ya gane koyarwannan ko daga wurin Allah ta zo, ko ko tawa ce ta kaina. 18 Ko wanene yake maganar kansa, yana neman darajar kansa kenan, amma ko wanene ya nemi darajar wanda ya aiko ni, wannan mutum mai gaskiya ne, babu rashin adalci a cikin sa. 19 Ba Musa ya baku dokoki ba? Amma duk da haka ba mai aikata dokokin. Me yasa ku ke so ku kashe ni? 20 Taron suka ba shi amsa, “Ka na da aljani. Wanene yake so ya kashe ka?” 21 Yesu ya amsa ya ce masu, “Nayi aiki daya, dukan ku kuna mamaki da shi. 22 Musa ya baku kaciya, {ba kuwa daga Musa take ba, amma daga kakannin kakanni ta ke}, kuma a ranar Asabar kukan yi wa mutum kaciya. 23 Idan mutum ya karbi kaciya ranar Asabar, domin kada a karya dokar Musa, don me kuka ji haushi na saboda na mai da mutum lafiyayye sarai ranar Asabar? 24 Kada ku yi shari'a ta ganin ido, amma ku yi shari'a mai adalci.” 25 Wadansun su daga Urushalima suka ce, “wannan ba shine wannan da suke nema su kashe ba?” 26 Kuma duba, yana magana a fili, sannan ba wanda ya ce da shi komai. Ba zai yiwu ba mahukunta su sani cewa wannan Kristi ne, ko ba haka ba? 27 da haka, mun san inda wannan mutum ya fito. Amma sa'anda Kristi za ya zo, ba wanda zai san inda ya fito.” 28 Yesu yayi magana da karfi a haikali, yana koyarwa ya na cewa, “Kun san ni kuma kun san inda na fito. Ban zo domin kaina ba, amma wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, ku kuwa baku san shi ba. 29 Ni na san shi domin daga wurinsa na fito, kuma shine ya aiko ni.” 30 Suna kokari su kama shi, amma ba wanda ya iya sa masa hannu domin sa'arsa ba ta yi ba tukuna. 31 Duk da haka wadansu dayawa a cikin taron suka bada gaskiya gare shi suka ce,”Sa'anda Kristi ya zo, zai yi alamu fiye da wadanda wannan mutum ya yi?” 32 Farisawa suka ji tattarmukan suna yin rada a kan wadannan abubuwa game da Yesu, Sai manyan malamai da Farisawa su ka aika jami'ai su kama shi. 33 Sa'annan Yesu yace ma su,” jimawa kadan ina tare ku, sa'annan in tafi wurin wanda ya aiko ni. 34 Za ku neme ni ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba.” 35 Yahudawa fa su ka cewa junan su, “Ina wannan mutum zai je inda ba za mu iya samun sa ba? Ko za ya tafi wurin Helinawa na warwatsuwa ya koyawa Helinawa? 36 Wace kalma ya ke fadi haka, 'za ku neme ni amma ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba'?” 37 To a rana ta karshe, babbar rana ta idin, Yesu ya mike ya yi magana da karfi cewa, “Idan kowa yana jin kishi, ya zo wuri na ya sha. 38 Shi wanda ya bada gaskiya gare ni kamar yadda nassi ya fadi, daga cikin sa rafukan ruwa na rai za su bulbulo.” 39 Amma ya fadi haka a kan Ruhu, wanda wadanda suka bada gaskiya gare shi za su karba; ba a ba da Ruhun ba tukuna, saboda ba a rigaya an daukaka Yesu ba. 40 Wadansu a cikin taron, sa'anda suka ji wadannan kalmomi, suka ce, “Wannan lallai annabi ne.” 41 Wadansu suka ce, “Wannan Almasihu ne.” Amma wadansu suka ce, “Almasihu zai fito daga Gallili ne.? 42 Ba nassi ya ce Almasihu zai fito daga cikin dangin Dauda daga Baitalami ba, daga kauyen da Dauda ya fito?” 43 Sai aka sami rabuwa a cikin taron saboda shi. 44 Da wadansun su sun kama shi, amma ba wanda ya sa masa hannu. 45 Sa'annan jami'an suka dawo wurin manyan Fristoci da Farisawa, wadanda suka ce,” me yasa ba ku kawo shi ba?” 46 Jami'an su ka amsa, “Ba mutumin da ya taba yin magana kamar haka.” 47 Farisawa suka amsa masu, “kuma an karkatar da ku? 48 Ko wani daga cikin mahukunta ya bada gaskiya gare shi, ko kuwa daga cikin Farisawa? 49 Amma wannan taro da basu san shari'a ba, la'anannu ne.” 50 Nikodimus ya ce masu, (shi wanda ya zo wurin Yesu da, daya daga cikin Farisawa), 51 “ Ko shari'armu bata hana hukunta mutum ba, sai ta ji daga gare shi ta kuma san abin da ya aikata ba?” 52 Suka amsa masa suka ce,”kai ma daga Galili ka fito? Ka yi bincike ka gani ba annanbin da zai fito daga Galili.” 53 Daga nan sai kowa ya tafi gidansa.