16
“Na fada maku wannan ne domin kada kuyi tuntube. Zasu fitar da ku daga majami'u. Amma, sa'a tana zuwa, wadda idan wani ya kasheku, zai yi zaton aikin Allah yake yi. Za suyi haka ne kuwa domin ba su san Uban ko ni ba. Na fada maku wadannan abubuwa ne domin in lokacin da zasu faru yayi, ku tuna na fada maku.” Ban fada maku wadannan abubuwa ba tun da farko, domin ina tare da ku. Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, 'Ina za ka?' Amma saboda na fada maku wadannan abubuwa, bakin ciki ya cika zuciyarku. Amma ina gaya maku gaskiya: zai fi ye maku in na tafi. Domin in ban tafi ba, Mai Ta'aziyya ba zai zo gare ku ba, in kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku. Idan kuwa ya zo, Mai Ta'aziyyar zai fadarkar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci. Game da zunubi, domin basu gaskata da ni ba, 10 Game da adalci, domin za ni wurin Uba, kuma ba za ku sake ganina ba, 11 game da hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulki duniyan nan hukunci. 12 “Akwai abubuwa da yawa da zan gaya maku, amma ba za ku iya fahimta a yanzu ba. 13 Saboda haka, sa'adda Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku a cikin dukan gaskiyar, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai fada, zai kuma sanar da ku al'amuran da zasu faru. 14 Zai daukaka ni, domin zai dauko abubuwa dake nawa ya sanar da ku. 15 Duk abinda Uba yake da shi, nawa ne. Domin wannan ne nace zai dauko abubuwa da yake nawa ya sanar da ku. 16 “Bayan dan lokaci kadan, ba zaku kara ganina kuma ba. bayan dan lokaci kadan kuma, zaku gan ni.” 17 Sai wadansu almajiransa sukace wa juna, “Me nene wannan da yake fadi mana, 'Bayan dan lokaci kadan ba zaku gan ni ba, bayan dan lokaci kadan kuma zaku gan ni?' da kuma, ' zan tafi wurin Uba'?” 18 Saboda haka sukace, “Me nene wannan da yake fada, 'Bayan dan lokaci kadan'? Bamu san abinda yake fada mana ba.” 19 Yesu kuwa ya ga suna so su tambaye shi, sai ya ce masu, “Wato kuna tambayar juna ne abinda nake nufi da cewa, “Bayan dan lokaci kadan ba zaku gan ni ba, bayan dan lokaci kadan kuma zaku gan ni'? 20 Hakika, hakika, ina gaya maku, zaku yi kuka da makoki, amma duniya za ta yi farin ciki, zaku cika da bakin ciki, amma bakin cikinku zai koma farin ciki. 21 Mace takan ji zafi lokacin da take nakuda don lokacin haihuwa ya zo. Amma da zarar ta haifi jinjirin nan, ba ta kara tunawa da zafin, domin ta na fariciki an haifi mutum a duniya. 22 To yanzu dai kuna bakin ciki, amma zan sake ganinku, kuma ba wanda zai iya kwace maku wannan farin ciki. 23 A rannan, ba zaku tambaye ni komai ba. Hakika hakika, ina gaya maku, komai kuka roki Uba a cikin sunana zai ba ku shi. 24 Harwa yau, ba ku roki komai cikin sunana ba. Ku roka, zaku karba, domin farin cikin ku ya zama cikakke.” 25 “Na fada maku wadannan abubuwa cikin karin magana. Amma sa'a tana zuwa da ba zan kara fada maku komai ba cikin karin magana, amaimakon haka zan gaya maku komai a sarari game da Uba. 26 A ranar nan, zaku yi roko a cikin sunana kuma bance maku zan yi addu'a ga Uba a madadinku ba, 27 domin Uba da kansa yana kaunarku, domin kun kaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito. 28 Daga wurin Uban na fito, kuma na shigo duniya. Har wa yau, kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.” 29 Almajiransa sukace, duba, “Yanzu kake magana a sarari, ba cikin karin magana ba! 30 Yanzu mun sani ka san komai, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito.” 31 Yesu ya amsa masu yace, “Ashe, yanzu kun gaskata? 32 Duba, sa'a na zuwa, I, sa'ar ta yi, da za a warwatsa ku, kowa ya koma gidansa, kuma ku bar ni ni kadai. Duk da haka kuwa ba ni kadai nake ba, domin Ubana yana tare da ni. 33 Na fada maku wannan ne domin a ciki na ku sami salama. A duniya kuna shan tsanani, amma ku karfafa: na yi nasara da duniya,”