19
Sai Bilatus yayi wa Yesu bulala. Sojojin kuwa suka saka rawanin kaya. Suka kuwa dora wa Yesu a kai suka sa mashi kaya irin na saurata. Suka zo wurin sa sukace, “Ranka ya dade, sarkin Yahudawa! sai suka nushe shi. Sai Bilatus ya sake fita waje yace masu, “Dubi, zan kawo maku mutumin domin ku sani ban same shi da wani laifi ba”, Yesu kuwa ya fito, da rawanin kaya da kaya irin na sarauta. Sai Bilatus yace “Ga mutumin nan”. Da manyan firistocin tare da yan majalisar suka ga Yesu, sai suka yi ta ihu suna cewa “A gicciye shi, A gicciye shi” Sai Bilatus yace masu, “ku dauke shi ku gicciye shi, ni kam ban same shi da wani laifi ba”. Sai Yahudawan sukace mashi, “Ai muna da shari'a, kuma bisa ga shari'ar ya cancanci mutuwa domin ya mai da kansa Dan Allah”. Da Bilatus ya ji wannan zance sai ya tsorata kwarai. Sai ya sake shiga fadar Gwamna, yace wa Yesu, “Daga ina ka fito?” amma Yesu bai amsa mashi ba. 10 Sai Bilatus yace masa “Ba zaka yi mani magana ba? Baka san ina da iko in sake ka ba, kuma in gicciye ka? 11 Yesu ya amsa masa, “Ai ba ka da iko a kaina sai dai in an baka daga sama, Saboda haka, wanda ya mika ni a gare ka shine mafi zunubi”. 12 Da jin haka, sai Bilatus yayi kokari a sake shi, amma sai Yahudawa suka tada murya sukace, “In ka saki mutumin nan, kai ba abokin Kaisar bane, duk wanda ya maida kansa sarki, ya sabawa Kaisar”. 13 Da Bilatus ya ji irin maganganunsu sai ya fito da Yesu waje ya kuma zauna akan kujeransa a inda ake kira “Dakalin shari'a,” a Yahudanci kuma, “Gabbata.” 14 To a ran nan ana shirye shiryen idin ketarewa, da misalin sa'a ta shidda kenan, wato tsakar rana, Bilatus yace wa Yahudawan “Ga sarkin ku!” 15 Su kuwa suka yi ihu, a tafi da shi, a tafi da shi, a gicciye shi, Bilatus yace masu “In gicciye sarkin ku? Sai manyan firistocin sukace “Ba mu da wani sarki sai Kaisar”. 16 Sai Bilatus ya mika Yesu domin su gicciye shi. 17 Sai suka tafi da Yesu, ya fito yana dauke da gicciyen zuwa wurin da ake kira “Wurin kwalluwa” da Yahudanci kuma “Golgota”. 18 Suka gicciye Yesu a wurin, tare da wasu mutum biyu, daya a kowane gefe, Yesu kuwa na tsikiya. 19 Bilatus kuwa ya rubuta wata alama a kan gicciyen, “YESU BANAZARE, SARKIN YAHUDAWA”. 20 Yahudawa da yawa kuwa suka karanta wannan alama domin wurin da aka gicciye Yesu yana kusa da Birnin. Alamar kuwa an rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da Helenanci. 21 Sai manyan firistocin yahudawa sukace wa Bilatus, kada ka rubuta sarkin Yahudawa, amma kace, 'wannan yace “Ni ne sarkin Yahudawa”'. 22 Bilatus kuwa ya amsa, “Abinda na rubuta na rubuta kenan.” 23 Bayan da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka yayyaga rigarsa kashi hudu, kowane soja da nasa, kashin, sai kuma alkyabbar. Alkyabbar kuwa bata da dinki an saka tane daga sama har kasa. 24 Sai sukace wa junansu, “Kada mu yaga alkyabbar, amma kuzo mu jefa kuri'a a kan ta mu gani ko wanene zai dauke ta, anyi haka ne domin a cika nassi cewa “Sun raba rigata a tsakaninsu, sun kuwa jefa kuri'a domin alkyabbata. 25 Sojojin suka yi wadannan abubuwa. Uwar Yesu, da 'yar'uwarta, da Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magadaliya. Wadannan mataye suna tsaye kusa da gicciyen Yesu. 26 Da Yesu ya ga mahaifiyarsa da almajirin nan da yake kauna tsaye kusa da juna, yace, “Mace, dubi, dan ki!” 27 Sai yace wa almajirin, “Dubi, mahaifiyarka!” Daga wannan sa'a almajirin ya dauke ta zuwa gidansa. 28 Bayan wannan Yesu, saboda ya san yanzu komai ya kammala, domin a cika nassin, sai yace “Ina jin kishi. 29 A gefensu kuma akwai gora cike da ruwan inabi mai tsami, sai suka tsoma soso a cikin ruwan inabin mai tsami suka daura a wata sanda sai suka mika masa a baki. 30 Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin, sai yace “An gama” Sai ya sunkuyar da kansa ya kuwa saki ruhunsa. 31 Sai Yahudawan, domin ranar shirye shirye ne, domin kada a bar jikunansu akan gicciye har ranar asabacin (domin asabacin rana ce mai muhimmanci), suka roki Bilatus ya kakkarye kafafunsu kuma ya saukar da su. 32 Sai sojojin suka zo suka karya kafafun mutum na farko da kuma mutum na biyun wadanda aka gicciye tare da Yesu. 33 Da suka iso kan Yesu sai suka tarar ya riga ya mutu, sai basu kuwa karya kafafunsa ba. 34 Duk da haka daya daga cikin sojojin ya soki kuibin shi da mashi, nan da nan sai jini da ruwa suka fito. 35 Wanda ya ga wannan, shi ya zama shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya sani cewa abinda ya fada gaskiya ne saboda ku ma ku gaskata. 36 Wadannan sun faru ne domin a cika nassi, “Babu ko daya daga cikin kasusuwansa da za'a karya”. 37 Kuma wani nassin yace, “Zasu dube shi wanda suka soka.” 38 Bayan wadannan abubuwa, Yusufu mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne (amma a boye saboda tsoron Yahudawa) ya roki Bilatus izini domin ya dauke jikin Yesu. Bilatus kuwa ya bashi izini, sai Yusufu yazo ya dauki jikin. 39 Nikodimu ma ya zo, wanda da farko ya zo wurin Yesu da daddare, ya kawo hadin man kamshi na mur da al'ul wajen nauyin awo dari. 40 Sai suka dauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin lillin tare da kayan kamshin nan, domin jana'iza bisa ga al'adar Yahudawa. 41 To a wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wani lambu, a cikin lambun kuma akwai sabon kabari wanda ba'a taba sa kowa ba. 42 Da yake ranar shirye shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuwa na kusa, sai suka sa Yesu a ciki.