Luka
1
Mutane da dayawa sun yi kokarin rubutu akan abubuwan da suka cika a tsakaninmu, kamar yanda suka danka mana su, wadanda tun daga farko suka zama shaidu da idanunsu kuma manzanni ne na sakon. Sabili da haka, ni ma, bayan da na yi bincike da kyau akan yanayin wadannan abubuwa tun da farko na ga ya yi kyau in rubuta wadannan abubuwa bi da bi ya mafi girmaTiyofilas. Ya zama haka domin ka san gaskiyar abin da aka koya maka ne. A cikin zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, akwai wani firist mai suna Zakariya, daga yankin Abija. Matarsa daga cikin yaya mata na zuriyar Haruna ce, kuma sunan ta Alisabatu ne. Dukan su biyu masu adalci ne a gaban Allah; marasa zargi a tafiyarsu cikin dukan dokoki da farilan Ubangiji. Amma ba su da da, domin Alisabatu ba ta haihuwa, kuma a wannan lokacin dukansu sun tsufa kwarai. Ya zama kuma a lokacin da Zakariya yana gaban Allah, yana yin hidimar sa ta firist bisa ga tsari da ka'idar aikinsa. Bisa ga al'adar zaben firist da zai yi hidima, an zabe shi ta wurin kuri'a ya shiga cikin haikalin Ubangiji domin ya kona turare. 10 Dukan taron Jama'a suna addu'a a waje a sa'adda ake kona turaren. 11 A lokacin, mala'ikan Ubangiji ya bayana a gare shi yana tsaye a gefen daman bagadi na turaren. 12 Zakariya ya firgita sa'adda ya gan shi; tsoro ya kama shi. 13 Amma mala'ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya, domin an ji addu'ar ka. Matar ka Alisabatu za ta haifa maka da. Za ka kira sunansa Yahaya. 14 Za ka yi murna da farin ciki, kuma da yawa za su yi murna da haifuwarsa. 15 Domin zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba zai sha ruwan inabi ba ko wani abu mai sa maye, kuma zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun daga cikin cikin mahaifiyarsa. 16 Kuma mutanen Isra'ila da yawa za su juya zuwa ga Ubangiji Allahnsu. 17 Zai yi tafiya a gaban Unbangiji a cikin ruhu da ikon Iliya. Zai yi haka domin ya juya zuciyar Ubanni zuwa ga 'ya'yansu, domin marasa biyayya su yi tafiya a cikin tafarkin adalai. Don ya shirya wa Ubangiji mutanen da aka shirya dominsa.” 18 Zakariya ya ce wa mala'ikan, “Ta yaya zan san wannan? Ga shi na tsufa kuma matata tana da shekaru da yawa.” 19 Mala'ikan ya amsa ya ce masa, “Nine Jibra'ilu, wanda ke tsaye a gaban Allah. An aiko ni in gaya maka wannan labari mai dadi. 20 Kuma duba, za ka zama bebe, ba za ka iya magana ba, sai ran da wadannan abubuwa suka cika. Ya zama haka domin ba ka gaskanta da kalmomina ba, wadanda za su cika a daidai lokacin.” 21 Sa'adda mutane suke jiran Zakariya. Sun yi mamaki yadda ya dauki lokaci sosai a cikin haikali. 22 Amma da ya fita, bai iya yin magana da su ba. Sun gane da cewa ya ga wahayi lokacin da yake cikin haikali. Ya ci gaba da yi masu alamu, ba ya magana. 23 Ya zama bayan da kwanakin hidimarsa suka kare, ya tafi gidansa. 24 Bayan kwanakin nan, matarsa Alisabatu ta samu juna biyu. Ta boye kanta har na watani biyar. Ta ce, 25 “Wannan shi ne abin da Allah ya yi mani da ya dube ni domin ya dauke kunyata a gaban jama'a.” 26 A cikin watan ta na shidda, an aiki Mala'ika Jibra'ilu daga wurin Allah zuwa wani birni a Galili mai suna Nazarat, 27 zuwa ga wata budurwa wanda aka ba da ita ga wani mutum mai suna Yusufu. Shi dan zuriyar Dauda ne, kuma ana kiran budurwar Maryamu. 28 Ya zo wurin ta ya ce, “A gaishe ki, ke da ki ke da tagomashi sosai! Ubangiji yana tare da ke. 29 Amma ta damu kwarai da wadannan kalmomi sai ta yi tunani ko wacce irin gaisuwa ce wannan. 30 Mala'ikan ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, domin kin samu tagomashi a wurin Allah. 31 Duba, za ki sami juna biyu, za ki haifi da. Za ki kira sunansa 'Yesu'. 32 Zai zama mai girma, kuma za a ce da shi Dan Allah Madaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi kursiyin ubansa Dauda. 33 Zai yi mulkin dukkan gidan Yakubu har abada, kuma mulkinsa ba shi da iyaka.” 34 Maryamu ta ce wa mala'ikan, “Yaya wannan zai faru, tun da shike ni ban san namiji ba?” 35 Mala'ikan ya amsa ya ce mata, “Ruhu Mai-tsarki zai sauko a kan ki, kuma ikon Madaukaki zai lullube ki. Sabili da haka, za a kira mai tsarkin da za ki haifa Dan Allah. 36 Ki kuma duba, ga 'yar'uwarki Alisabatu ta samu juna biyu a tsufanta. Watannin ta shida kenan, ita wadda aka kira ta bakarariya. 37 Gama babu abin da ba shi yiwuwa a wurin Allah.” 38 Maryamu ta ce, “To, ni baiwar Ubangiji ce. Bari ya faru da ni bisa ga sakonka.” Sai mala'ikan ya bar ta. 39 Sai Maryamu ta tashi da sauri a cikin kwanakin nan, zuwa kasa mai duwatsu, zuwa wani birni a Yahudiya. 40 Ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Alisabatu. 41 Ya zama sa'adda Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, sai dan da ke cikinta ya yi tsalle, an cika Alisabatu kuma da Ruhu Mai Tsarki. 42 Ta daga murya, ta ce, “Mai albarka kike a cikin mata, kuma mai albarka ne dan cikinki. 43 Kuma don me ya faru da ni da uwar Ubangijina ta ziyarce ni? 44 Kuma duba, da na ji karar gaisuwan ki sai dan ciki na ya yi tsalle domin murna. 45 Kuma mai albarka ce wadda ta gaskanta cewa abubuwan da aka alkawarta mata daga wurin Ubangiji za su cika. 46 Maryamu ta ce, “Zuciyata ta yabi Ubangiji, 47 kuma ruhu na ya yi murna da Allah mai ceto na.” 48 Domin ya dubi kaskancin baiwarsa. Duba, daga yanzu, dukkan tsararraki za su ce da ni mai albarka. 49 Domin shi madaukaki ya yi mani manyan abubuwa, kuma sunansa Mai Tsarki ne. 50 Jinkansa ya tabbata daga tsara zuwa tsara wadanda suke girmama shi. 51 Ya nuna karfinsa da hannuwansa; ya warwatsa ma su girman kai game da tunanin zuciyarsu. 52 Ya nakasar da magada daga kursiyoyinsu, ya kuma fifita nakasassu. 53 Ya ciyar da mayunwata da abubuwa masu kyau, amma ya aiki attajirai wofi. 54 Ya ba da taimako ga bawan sa Isra'ila, domin ya tuna ya kuma nuna jinkai 55 (kamar yanda ya fada wa ubaninmu) ga Ibrahim da zuriyarsa har abada.” 56 Maryamu ta zauna da Alisabatu tsawon watanni uku sai ta koma gidanta. 57 Da lokaci yayi da Alisabatu za ta haifi danta, ta kuma haifi da namiji. 58 Makwabtanta da 'yan'uwanta sun ji cewa Ubangiji ya ribanbanya jinkansa akanta, sai suka yi murna tare da ita 59 Ya zama akan rana ta takwas, sun zo domin a yi wa yaron kaciya. Da sun kira sunansa “Zakariya” kamar sunan ubansa, 60 amma mahaifiyarsa ta amsa ta ce, “A'a, za a kira shi Yahaya.” 61 Suka ce mata, “Babu wani a cikin danginku wanda ake kira da wannan suna.” 62 Sun nuna alama ga ubansa bisa ga yanda ya ke so a rada masa suna. 63 Ubansa ya nemi a ba shi allon rubutu, sai ya rubuta, “Sunansa Yahaya.” Dukan su suka yi mamaki kwarai da wannan. 64 Nan take, sai bakinsa ya bude kuma harshensa ya saki. Ya yi magana ya kuma yabi Allah. 65 Tsoro ya kama dukan wadanda suke zama kewaye da su. Sai labarin ya bazu cikin dukan kasar duwatsu ta Yahudiya. 66 Kuma dukan wadanda suka ji su, sun ajiye su a cikin zuciyarsu, suna cewa, “To me wannan yaro zai zama ne?” Domin hannun Ubangiji yana nan tare da shi. 67 Ruhu Mai-tsarki ya cika mahaifinsa Zakariya sai ya yi anabci cewa, 68 “Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra'ila domin ya zo ya taimaki mutanen sa kuma ya yi aikin ceto domin su.” 69 Ya ta da kahon ceto dominmu daga gidan bawansa Dauda, daga zuriyar Dauda bawansa, 70 kamar yadda ya fada ta bakin annabawansa tsarkaka tun zamanin zamanai. 71 Zai kawo mana ceto daga magabtan mu da kuma daga hannun makiyanmu. 72 Zai yi haka domin ya nuna jinkai ga ubaninmu ya kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki, 73 rantsuwar da ya fada wa ubanmu Ibrahim. 74 Ya rantse zai yardar mana, bayan da an kubutar da mu daga hannun makiyanmu, mu bauta masa ba tare da tsoro ba, 75 a cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakin ranmu. 76 I, kai kuma, yaro, za a kira ka annabi na Madaukaki, domin za ka tafi gaban fuskar Ubangiji ka shirya hanyoyinsa, ka shirya mutane domin zuwansa, 77 domin ba mutanensa ilimin ceto ta wurin gafarar zunubansu. 78 Wannan zai faru ne domin girman jinkan Allahnmu, sabili da hasken rana daga bisa za ya zo wurinmu, 79 domin haskakawa akan wadanda ke zaune a cikin duhu da kuma cikin inuwar mutuwa. Zai yi hakan nan domin ya kiyaye kafafunmu zuwa hanyar salama. 80 Yaron ya yi girma ya kuma zama kakkarfa a cikin ruhu, yana kuma cikin jeji sai ranar bayyanuwarsa ga Isra'ila.