Matiyu
1
Littafin asalin Yesu Almasihu Dan Dauda, Dan Ibrahim. Ibrahim shine mahaifin Ishaku, Ishaku shine mahaifin Yakubu, Yakubu shine mahaifin Yahuza da 'yan'uwansa. Yahuza shine mahaifin Farisa da Zera, ta wurin Tamar. Farisa kuma shine mahaifin Hasruna, Hasruna kuma shine mahaifin Aram. Aram shine mahaifin Amminadab, Amminadab shine mahaifin Nashon, Nashon shine mahaifin Salmon. Salmon shine mahaifin Bo'aza ta wurin Rahab, Bo'aza shine mahaifin Obida ta wurin Rut. Obida shine mahaifin Yesse, Yesse shine mahaifin sarki Dauda. Sarki Dauda shine mahaifin Sulaimanu ta wurin matar Uriya. Sulaimanu shine mahaifin Rehobo'am, Rehobo'am shine mahaifin Abija, Abija shine mahaifin Asa. Asa shine mahaifin Yehoshafat, Yehoshafat shine mahaifin Yoram, Yoram kuma shine mahaifin Uziya. Uziya shine mahaifin Yotam, Yotam shine mahaifin Ahaz, Ahaz shine mahaifin Hezekiya. 10 Hezekiya shine mahaifin Manassa, Manassa shine mahaifin Amon, sannan Amon shine mahaifin Yosiya. 11 Yosiya shine mahaifin Yekoniya da 'yan'uwansa, dai dai locacin da aka kwashe su zuwa kasar Babila. 12 Bayan kwasar su zuwa kasar Babila, Yekoniya shine mahaifin Sheyaltiyel, Sheyaltiyel shine mahaifin Zarubabel. 13 Zarubabel shine mahaifin Abihudu, Abihudu shine mahaifin Eliyakim, sannan Eliyakim shine mahaifin Azuru. 14 Azuru shine mahaifin Saduku. Saduku shine mahaifin Akimu, sannan Akimu shine mahaifin Aliyudu 15 Aliyudu shine mahaifin Ali'azara, Ali'azara shine mahaifin Matana, sannan Matana shine mahaifin Yakubu. 16 Yakubu shine mahaifin Yusufu maigidan Maryamu, wadda ta wurin ta ne aka haifi Yesu, wanda ake ce da shi Almasihu. 17 Tun daga Ibrahim zuwa Dauda, an yi tsara goma sha hudu ne, daga Dauda zuwa lokacin da aka kwashe su zuwa Babila, tsara goma sha hudu ne, sannan daga lokacin da aka kwashe su zuwa Babila zuwa Almasihu tsara goma sha hudu ne 18 Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu ta kasance. Mahaifiyarsa, Maryamu, tana tashi da Yusufu, amma kafin su yi aure, sai aka same ta da juna biyu ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 19 Mijinta, Yusufu, adalin mutum ne, amma ba ya so ya kunyatar da ita a sarari. Sai ya yi shawara ya sake ta a asirce. 20 Yana cikin tunanin wadannan al'amura, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, “Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi. 21 Za ta haifi Da, za ka kira sunansa Yesu, domin za ya ceci mutanensa daga zunubansu.” 22 Duk wannan ya faru ne domin a cika abinda aka fada ta bakin annabin, cewa, 23 “Duba, budurwa za ta sami juna biyu sannan za ta haifi da, za su kira sunansa Immanuel”-ma'ana, “Allah tare da mu.” 24 Yusufu ya farka daga barci, ya yi kamar yadda mala'ikan Ubangiji ya umarce shi, sai ya dauke ta a matsayin matarsa. 25 Amma Yusufu bai sadu da ita ba sai bayan da ta haifi da. Ya kira sunansa Yesu.