2
Ruhu Mai Tsarki ya zo a Fentekos
Da ranar Fentekos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya. Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune. Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya.
To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya. Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa. Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa, “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne? To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa? Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya, 10 Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma 11 (Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa, mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!” 12 A ruɗe kuma cike da mamaki, suka tambayi junansu cewa, “Mene ne wannan yake nufi?”
13 Duk da haka waɗansu suka yi musu ba’a suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.”
Bitrus ya yi wa taron jawabi
14 Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, “’Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa. 15 Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai! 16 A’a, ai, abin da aka yi magana ta bakin annabi Yowel ke nan cewa,
17 “Allah ya ce, ‘A kwanakin ƙarshe,
zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane.
’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci,
samarinku za su ga wahayoyi,
dattawanku kuma za su yi mafarkai.
18 Kai, har ma a kan bayina, maza da mata,
zan zubo Ruhuna a waɗancan kwanaki,
za su kuwa yi annabci.
19 Zan nuna abubuwan banmamaki a sararin sama
da alamu a nan ƙasa,
jini da wuta da kuma hauhawan hayaƙi.
20 Za a mai da rana duhu,
wata kuma ya zama jini,
kafin zuwa rana mai girma da kuma ta ɗaukaka ta Ubangiji.
21 Kuma duk wanda ya kira
bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.’*
22 “Mutanen Isra’ila, ku saurari wannan. Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin mu’ujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani. 23 An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye. 24 Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya ’yantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi. 25 Dawuda ya yi faɗi game da shi cewa,
“ ‘Kullum ina ganin Ubangiji a gabana.
Gama yana a hannuna na dama,
ba zan jijjigu ba.
26 Saboda haka, zuciyata na farin ciki, harshena kuma na murna,
jikina kuma zai kasance da bege,
27 gama ba za ka bar ni cikin kabari ba,
ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.
28 Ka sanar da ni hanyoyin rai,
za ka cika ni da farin ciki a gabanka.’
29 “’Yan’uwa, zan iya tabbatar muku gabagadi cewa kakanmu Dawuda ya mutu aka kuma binne shi, kabarinsa kuwa yana a nan har yă zuwa yau. 30 Amma shi annabi ne ya kuma san abin da Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa zai ɗora ɗaya daga cikin zuriyarsa a kan gadon sarautarsa. 31 Ganin abin da yake gaba, ya yi magana a kan tashin Kiristi daga matattu cewa, ba a bar shi a kabari ba, jikinsa kuma bai ruɓa ba. 32 Allah ya tashe wannan Yesu zuwa rai, mu kuwa duk shaidu ne ga wannan. 33 An ɗaukaka shi zuwa ga hannun dama na Allah, ya karɓi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga Uba, ya kuma zubo abin da yanzu kuke gani kuke kuma ji. 34 Gama Dawuda bai hau zuwa sama ba, duk da haka ya ce,
“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
“Zauna a hannun damana,
35 sai na sa abokan gābanka
su zama matashin sawunka.” ’
36 “Saboda haka bari dukan Isra’ila su tabbatar da wannan. Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi.”
37 Sa’ad da mutane suka ji wannan, sai suka soku a zuci sai suka ce wa Bitrus da sauran manzanni, “’Yan’uwa, me za mu yi?”
38 Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki. 39 Alkawarin dominku ne da ’ya’yanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa, domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira.”
40 Da waɗansu kalmomi masu yawa ya gargaɗe su; ya kuma roƙe su cewa, “Ku ceci kanku daga wannan lalataccen zamani.” 41 Waɗanda suka yarda da saƙonsa kuwa aka yi musu baftisma, a ranar kuwa yawansu ya ƙaru da mutum kusan dubu uku.
Zumuncin masu bi
42 Suka ba da kansu ga koyarwar manzanni da kuma ga zumunci, ga gutsuttsura burodin da kuma ga addu’a. 43 Kowa ya cika da tsoro, manzannin kuwa suka aikata abubuwan banmamaki da alamu masu yawa. 44 Dukan masu bi suna tare, suna kuma mallakar kome tare. 45 Suka dinga sayar da ƙaddarorinsu da kayayyakinsu, suka ba wa kowa gwargwadon bukatarsa. 46 Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya, 47 suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto.
* 2:21 Yow 2.28-32 2:28 Zab 16.8-11 2:35 Zab 110.1