5
Makoki da kuma kira ga tuba
1 Ku ji wannan magana, ya gidan Isra’ila, ina makokin nan dominku.
2 “Budurwa Isra’ila ta fāɗi,
ba za tă ƙara tashi ba,
an yashe ta a ƙasarta,
ba wanda zai ɗaga ta.”
3 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce,
“Birnin da ta fitar da masu ƙarfi dubbai don Isra’ila
guda ɗari kaɗai za su dawo;
garin da ya fitar da masu ƙarfi ɗari kuwa
goma kaɗai za su dawo.”
4 Ga abin da Ubangiji ya ce wa gidan Isra’ila.
“Ku neme ni ku rayu;
5 kada ku nemi Betel,
kada ku je Gilgal,
kada ku yi tafiya zuwa Beyersheba.
Gama ba shakka Gilgal za tă tafi bauta,
za a kuwa mai da Betel ba kome ba.”
6 Ku nemi Ubangiji ku kuma rayu,
ko kuwa zai ratsa yă share gidan Yusuf kamar wuta;
zai cinye
Betel kuwa ba zai sami wanda zai kashe ta ba.
7 Ku ne masu mai da gaskiya ta koma ɗaci
ku kuma zubar da adalci.
8 (Shi wanda ya yi Taurarin nan da ake ce Kaza da ’Ya’yanta da kuma Mai Farauta da Kare,
wanda ya mai da duhu ya zama haske
ya kuma baƙanta rana ta zama dare,
yakan kwashe ruwan teku
ya zubar a ƙasa,
Ubangiji ne sunansa,
9 yakan kawo hallaka a mafaka mai ƙarfi
yakan kuma mai da birnin mai katanga ya zama kufai).
10 Ba ku son mai yin gaskiya a ɗakin shari’a
kuna ƙin mai faɗar gaskiya.
11 Kuna matsa wa matalauta
kuna sa su dole su ba ku hatsi.
Saboda haka, ko da yake kun gina gidajen duwatsu,
ba za ku zauna a cikinsu ba;
ko da yake kun nome gonaki masu kyau,
ba za ku sha ruwan inabinsu ba.
12 Gama na san yawan laifofinku
da kuma girman zunubanku.
Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci
kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa.
13 Saboda haka mai hankali yakan yi shiru a lokuta kamar haka,
gama lokutan mugaye ne.
14 Ku yi nagarta, ba mugunta ba;
don ku rayu
sa’an nan Ubangiji Allah Maɗaukaki zai kasance da ku,
kamar yadda kuka ce zai yi.
15 Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta;
ku dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunan shari’a.
Mai yiwuwa Ubangiji Allah Maɗaukaki zai ji tausayin
raguwar Yusuf.
16 Saboda haka ga abin da Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa,
“Za a yi kururuwa a dukan tituna
a kuma yi kuka don azaba a dukan wuraren da jama’a sukan taru.
Za a yi kira ga manoma su yi kuka
masu makoki kuma su yi kuka.
17 Za a yi kuka a dukan gonakin inabi,
gama zan ratsa a cikinku,”
in ji Ubangiji.
Ranar Ubangiji
18 Kaitonku masu son
ganin ranar Ubangiji!
Don me kuke son ganin ranar Ubangiji?
Za a duhunta ranan nan, ba haske ba.
19 Za ku zama kamar mutanen da suka guje wa zaki
sai suka fāɗa a hannun beyar,
ko kuma kamar wanda ya shiga gida
ya dāfa hannu a bango
sai maciji ya sare shi.
20 Ashe, ranar Ubangiji ba duhu ba ce, a maimakon haske,
duhu wuluk, ba tare da ko ɗan haske ba.
21 “Na ƙi, ina kuma ƙyamar bukukkuwanku na addini;
ba na son ganin tarurrukanku.
22 Ko da kun kawo mini hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na hatsi,
ba zan karɓa ba.
Ko da kun kawo zaɓaɓɓun hadayu na zumunta,
ba zan ɗauke su a bakin kome ba.
23 Ku tashi daga nan da surutan waƙoƙinku!
Ba zan saurari kaɗe-kaɗe da bushe bushenku ba.
24 Amma bari gaskiya ta kwararo kamar kogi,
adalci kuma kamar rafin da ba ya taɓa bushewa!
25 “Kun kawo mini hadayu da sadakoki
shekaru arba’in a cikin jeji, ya ku gidan Isra’ila?
26 Kun ɗaga masujadar sarkinku,
siffofin gumakanku,
tauraron allahnku,
wanda kuka yi wa kanku.
27 Saboda haka zan tura ku zaman bauta gaba da Damaskus,”
in ji Ubangiji, wanda sunansa ne Allah Mai Iko.