7
Fāri, wuta, da igiyar gwaji
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji yana shirya cincirindon fāri bayan da aka ƙarasa yankan rabon hatsin da yake na sarki, hatsi na biyu kuma yake tohuwa. Sa’ad da suka cinye kome, sai na yi kira, na ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, ka gafarta! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”
Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa.
“Wannan ba zai faru ba,” in ji Ubangiji.
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji Mai Iko Duka yana shirin hukunta da wuta; wutar ta ƙone teku ta kuma ƙone ƙasa. Sai na yi kira, na ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, ina roƙonka ka dakata! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”
Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa.
“Wannan ma ba zai faru ba,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
 
Ga abin da ya nuna mini. Ubangiji yana tsaye kusa da bangon da aka gina, bisa ga awon igiyar gwada gini, da kuma magwaji a hannunsa. Sai Ubangiji ya tambaye ni, “Me kake gani, Amos?”
Sai na amsa, “Igiyar gwada gini.”
Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Duba, zan sa igiyan nan a cikin mutanena Isra’ila; ba zan ƙara barinsu ba.
“Za a hallakar da wuraren sujada na Ishaku
kuma tsarkakan wurare na Isra’ila za su zama kango;
da takobina zan tayar wa gidan Yerobowam.”
Amos da Amaziya
10 Sai Amaziya firist na Betel ya aika da saƙo zuwa wurin Yerobowam sarkin Isra’ila. “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a tsakiyar Isra’ila. Ƙasar ba za tă iya ɗauka abubuwan da yake faɗi ba. 11 Gama ga abin da Amos yake cewa,
“ ‘Yerobowam zai mutu ta wurin takobi,
kuma tabbatacce Isra’ila za su tafi zaman bauta,
nesa da ainihin ƙasarsu.’ ”
12 Sai Amaziya ya ce wa Amos, “Tafi daga nan, mai duba kawai! Koma ƙasar Yahuda. Ka nemi abin zaman garinka a can ka kuma yi annabcinka a can. 13 Kada ka ƙara yin annabci a Betel, gama nan wuri mai tsarki ne na sarki da kuma haikalin ƙasar.”
14 Amos ya amsa wa Amaziya, “Ni ba annabi ba ne ko ɗan annabi, amma ni makiyayi ne, kuma ina lura da itatuwan al’ul. 15 Amma Ubangiji ya ɗauke ni daga kiwon dabbobi ya ce mini, ‘Je ka, ka yi wa mutanena Isra’ila annabci.’ 16 Yanzu fa, sai ka ji maganar Ubangiji. Ka ce,
“ ‘Kada in yi annabci a kan Isra’ila,
kuma in daina yin wa’azi a kan gidan Ishaku.’
17 “Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce,
“ ‘Matarka za tă zama karuwa a cikin birni,
kuma da takobi za a kashe ’ya’yanka maza da mata.
Za a auna ƙasarka a kuma raba ta,
kai kuma za ka mutu a ƙasar arna.*
Ba shakka Isra’ila za su tafi zaman bauta,
nesa da ainihin ƙasarsu.’ ”
* 7:17 Da Ibraniyanci marasa tsabta