16
Bayarwa saboda mutanen Allah
1 To, game da tara kuɗi domin taimakon mutanen Allah, ku yi abin da na gaya wa ikkilisiyoyin Galatiyawa.
2 A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba.
3 In kuwa na iso sai in ba da wasiƙun gabatarwa ga mutanen da kuka amince da su, in kuma aike su da taimakonku zuwa Urushalima.
4 In kuma ya dace in tafi, to, sai su tafi tare da ni.
Roƙona
5 Bayan na zazzaga Makidoniya, zan zo wurinku, domin zan ratsa ta Makidoniya.
6 Wataƙila zan ɗan jima a wajenku, ko ma in ci damina a can, domin ku yi mini rakiya a tafiyata, duk inda za ni.
7 Ba na so in gan ku yanzu in wuce kawai, ina fata zan yi ’yan kwanaki tare da ku, in Ubangiji ya yarda.
8 Sai dai zan kasance a Afisa har lokacin Fentekos,
9 domin an buɗe mini wata hanya mai fāɗi don aiki mai amfani, ko da yake akwai mutane da yawa masu gāba da ni.
10 In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi.
11 Kada fa wani yă ƙi karɓansa. Ku sallame shi lafiya, domin yă koma wurina. Ina duban hanyarsa tare da ’yan’uwa.
12 Batun ɗan’uwanmu Afollos kuwa, na roƙe shi sosai yă zo wurinku tare da ’yan’uwa. Bai so zuwa yanzu ba, amma zai zo in ya sami zarafi.
13 Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi.
14 Ku yi kome da ƙauna.
15 Kun san cewa iyalin gidan Istifanas ne suka fara tuba a Akayya. Sun kuma ba da kansu ga yi wa tsarkaka hidima. Ina roƙonku ’yan’uwa,
16 ku ba da kanku ga irin waɗannan, ga kuma kowa da ya haɗa hannu a aikin, yana kuma faman a cikinsa.
17 Na yi farin ciki da isowar Istifanas, Fortunatus da Akaikus, domin sun biya bukatar da ba ku iya biya ba.
18 Gama sun wartsake ruhuna da kuma naku. Ya kamata ku girmama irin waɗannan mutane.
Gaisuwa ta ƙarshe
19 Ikkilisiyoyin da suke a lardin Asiya suna gaisuwa.
Akwila da Firiskila suna gaishe ku sosai cikin Ubangiji, haka ma ikkilisiyar da takan taru a gidansu.
20 Dukan ’yan’uwa a nan suna gaisuwa.
Ku gai da juna da sumba mai tsarki.
21 Ni, Bulus nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna.
22 Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji, la’ana ta zauna a kansa. Zo, ya Ubangiji!
23 Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da ku.
24 Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙaunata cikin Kiristi Yesu. Amin.