5
A yi waje da ɗan’uwa mai halin lalata
1 Ana ba da labari cewa ana lalata a cikinku, irin da ba a ma samu a cikin masu bautar gumaka. Har mutum yana kwana da matar mahaifinsa.
2 Har ya zama muku abin taƙama! Ashe, bai kamata ku cika da baƙin ciki ku kuma daina zumunci da mutumin da yake aikata wannan ba?
3 Ko da yake ba na nan tare da ku cikin jiki, ina tare da ku a cikin ruhu. Na riga na yanke wa wanda ya aikata wannan hukunci, kamar dai ina tare da ku.
4 Saboda haka sa’ad da kun taru ikon Ubangijinmu Yesu kuma yana nan, ni ma ina tare da ku.
5 Ku miƙa irin wannan mutum ga Shaiɗan, don a hallaka halin nan na mutuntaka, ruhunsa kuma yă sami ceto a ranar da Ubangiji zai dawo.
6 Ku daina taƙama. Ba ku san cewa ɗan ƙanƙanin yisti ne yakan sa dukan curin burodi yă kumbura ba?
7 Ku kawar da tsohon yisti don ku zama kamar sabon curi da aka yi babu yisti yadda dai kuke. Gama an miƙa Kiristi Ɗan Ragon Bikin Ƙetarewarmu.
8 Saboda haka, sai mu kiyaye Bikin ba da burodi mai tsohon yisti ba, ba kuma da yisti na ƙeta da mugunta ba, sai dai da burodi marar yisti na sahihanci da na gaskiya.
9 Na rubuta muku cikin wasiƙata, kada ku yi haɗa kai da masu aikin lalata.
10 Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai yă zama dole ku fita daga duniya.
11 Yanzu dai ina rubuta muku cewa kada ku haɗa kai da duk mai kiran kansa ɗan’uwa, amma yana fasikanci, ko kwaɗayi, ko bautar gumaka, ko ɓata suna, ko mashayi, ko mazambaci. Kada ku ko ci abinci da irin wannan mutum.
12 Me zai kai yin hukunci ga waɗanda ba ’yan ikkilisiya ba. Ai, waɗanda suke ’yan ikkilisiya ne za ku hukunta.
13 Allah zai hukunta waɗanda ba namu ba. “Ku yi waje da irin mugun mutumin nan daga cikinku.”