13
Gargaɗin ƙarshe
Wannan za tă zama ziyarata ta uku a wurinku ke nan. “Dole a tabbatar da kowace magana ta bakin shaidu biyu ko uku.”* Na riga na yi muku gargaɗi sa’ad da nake tare da ku a zuwana na biyu. Yanzu da ba na nan tare da ku, ina maimaita irin gargaɗin nan domin in na zo ba wanda zai kuɓuce wa horon nan, da yake kuna neman tabbaci cewa Kiristi yana magana ta wurina ne. To, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku. Ko da yake tabbatacce an gicciye shi cikin rashin ƙarfi, duk da haka, yana rayuwa bisa ga ikon Allah. Haka mu ma marasa ƙarfi ne a cikinsa, amma ta wurin ikon Allah za mu rayu tare da shi don mu yi muku hidima.
Ku gwada kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya; ku auna kanku. Ashe, ba ku san cewa Kiristi Yesu yana cikinku ba? Sai ko in kun fāɗi gwajin. Ina fata za ku gane cewa ba mu fāɗi gwajin ba. Muna addu’a ga Allah kada ku aikata wani laifi. Ba don mutane su gani cewa mun ci gwajin ba ne, a’a, sai dai don ku yi abin da yake daidai, ko da yake zai zama kamar mun fāɗi gwajin ne. Kai, ba dama mu saɓa wa gaskiya, sai dai mu bi bayan gaskiyar. Murna muke sa’ad da ba mu da ƙarfi, ku kuwa kuna da ƙarfi. Addu’armu ita ce, ku zama cikakku. 10 Shi ya sa nake rubuta waɗannan abubuwa, sa’ad da ba na nan tare da ku, domin sa’ad da na zo, kada yă zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.
 
Gaisuwa ta ƙarshe
11 A ƙarshe ’yan’uwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku.
 
12 Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki.
13 Dukan tsarkaka suna gaishe ku.
 
14 Alherin Ubangiji Yesu Kiristi, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka.
* 13:1 M Sh 19.15