10
Alluna kamar na farko
(Fitowa 34.1-10)
A lokacin Ubangiji ya ce mini, “Ka sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ka haura wurina a kan dutse. Ka kuma yi akwatin katako.* Ni kuwa zan yi rubutu a kan allunan nan biyu, kalmomin da suke a alluna na farko, waɗanda ka farfashe. Za a ajiye su a cikin akwatin.”
Sai na yi akwatin da itacen ƙirya, na kuma sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, sai na haura dutse da alluna biyun a hannuwana. Ubangiji kuwa ya sāke yin rubutu a waɗannan alluna abin da ya rubuta a allunan farko, wato, Dokoki Goma da ya furta a kan dutse a tsakiyar wuta, a ranar da mutane suka taru. Sai Ubangiji ya ba ni su. Sa’an nan na sauko daga dutsen, na kuma ajiye allunan a cikin akwatin da na yi, yadda Ubangiji ya umarce ni, kuma suna can a yanzu.
(Ƙidaya 20.22-29)
(Isra’ilawa suka kama hanya daga rijiyoyin Beyerot Bene Ya’akan zuwa Mosera. A can Haruna ya rasu, aka kuma binne shi. Sai Eleyazar ɗansa ya gāje shi a matsayin firist. Daga can suka tashi zuwa Gudgoda, daga Gudgoda kuma suka tafi Yotbata, ƙasa mai rafuffukan ruwa. A lokacin Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi don su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yin masa hidima, su kuma sa albarka a cikin sunansa, yadda suke yi har wa yau. Shi ya sa Lawiyawa ba su da rabo, ko gādo a cikin ’yan’uwansu; Ubangiji ne gādonsu yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.)
(Fitowa 34.9,10,27-29)
10 To, na kasance a kan dutse yini arba’in da dare arba’in kamar yadda dā na yi da farko. Ubangiji kuwa ya saurare ni a wannan lokaci kuma. Ba nufinsa ba ne yă hallaka ku. 11  Ubangiji ya ce mini, “Ka sauka, ka jagoranci mutanen a hanyarsu, domin su shiga, su kuma mallaki ƙasar da na rantse wa kakanninsu, zan ba su.”
Ku ji tsoron Ubangiji
12 Yanzu fa, ya Isra’ila, mene ne Ubangiji Allahnku yake so a gare ku, in ba ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, 13 ku kuma kiyaye umarnan Ubangiji da kuma ƙa’idodinsa da nake ba ku a yau don amfaninku ba?
14 Sammai, har da sama sammai, da duniya, da kome da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne. 15 Duk da haka Ubangiji ya ƙaunaci kakanninku, ya kuma zaɓe ku, ku zuriyarsu, a bisa dukan al’ummai, yadda yake a yau. 16 Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai. 17 Gama Ubangiji Allahnku ne Allahn alloli da Ubangijin iyayengiji, Allah mai girma, mai ƙarfi da kuma mai banrazana, wanda ba ya sonkai, ba ya cin hanci. 18 Yakan tsare marayu da gwauraye, yana ƙaunar baƙon da yake zama a cikinku, yana ba su abinci da tufafi. 19 Sai ku ƙaunaci baƙi, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar. 20 Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku kuma bauta masa. Ku manne masa, ku kuma yi rantsuwarku da sunansa. 21 Shi ne abin yabonku; shi ne Allahnku, wanda ya aikata muku waɗancan manya abubuwa banmamaki masu banrazanar da kuka gani da idanunku. 22 Kakanninku da suka gangara zuwa Masar, su saba’in ne, yanzu kuwa Ubangiji Allahnku ya sa kuka ƙaru, kuka zama kamar taurari a sama.
* 10:1 Wato, akwatin alkawari