5
Ka ji tsoron Allah
Ka lura da matakanka sa’ad da ka tafi gidan Allah. Ka je kusa don ka saurara a maimakon miƙa hadaya kamar wawaye, waɗanda ba su san sun yi laifi ba.
Kada ka yi subul da bakinka,
kada zuciyarka tă yi garajen
furta wani abu a gaban Allah.
Allah yana sama
kai kuma kana duniya,
saboda haka, kada kalmominka su zama da yawa.
Kamar yadda son cika buri yakan zo sa’ad da kana da yawan damuwa,
haka jawabin wawa yake sa’ad da yake yawan magana.
Sa’ad da ka yi alkawari ga Allah, kada ka ɓata lokaci wajen cika shi. Ba ya jin daɗin wawaye; ka cika alkawarinka. Gara kada ka yi alkawari, da ka yi amma ba ka cika ba. Kada ka bar bakinka ya kai ga yin zunubi. Kada kuma ka kai ƙara wurin ɗan saƙon haikali cewa, “Alkawarin da na yi kuskure ne.” Me ya sa Allah yake fushi a kan abin da ka faɗa har yă lalatar da aikin hannuwanka? Yawan buri da yawan magana ba su da amfani. Saboda haka, ka ji tsoron Allah.
Arziki ba shi da amfani
In ka ga ana zaluntar matalauta a wani yanki, ba a yin adalci, ana kuma tauye hakki, kada ka yi mamakin waɗannan abubuwa; domin akwai wani jami’in da yake bisa da wani, a bisansu biyu kuwa akwai wani. Kowa yakan amfana da bunkasar amfanin ƙasa, sarki kansa yana samun riba daga gonaki.
10 Duk mai ƙaunar kuɗi ba ya samun isashe;
duk ma ƙaunar dukiya ba ya ƙoshi da abin da yake samu.
Wannan ma ba shi da amfani.
 
11 Kamar yadda kaya suke haɓaka,
haka ma masu amfani da su.
Kuma wane amfani ne suke ga mai shi
in ba ciyar da idanunsa a kansu ba?
 
12 Barcin ma’aikaci daɗi gare shi,
ko yă ci kaɗan ko da yawa,
amma yalwar mai arziki
ba ta barinsa yă iya yin barci.
13 Na ga wani mugun abu a duniya,
arzikin da aka ajiye don yă cuce mai shi,
14 ko kuwa dukiyar da ta ɓace ta wata hasara,
har ya zama sa’ad da ya haifi ɗa,
babu abin da ya bar masa.
15 Tsirara mutum yakan fito daga cikin mahaifiyarsa,
kuma kamar yadda ya fito, haka zai koma.
Ba ya ɗaukan kome daga wahalarsa
da zai riƙe a hannunsa.
16 Wannan ma mugun abu ne,
Yadda mutum ya zo, haka zai koma,
to, wace riba ce ya ci,
da yake ya yi wahalar iska ce kawai?
17 Duk rayuwarsa ya ci abinci a cikin duhu,
da ɓacin rai mai tsanani, da azaba, da fushi.
18 Sa’an nan na gane cewa abu mai kyau ne, daidai ne kuma mutum yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗin aikin da ya yi a ’yan kwanakin da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum daga faman wahalarsa a duniya a cikin ’yan kwanakin da Allah ya ba shi a duniya, gama wannan shi ne rabonsa. 19 Ban da haka ma, sa’ad da Allah ya ba wa mutum dukiya da wadata, ya kuma ba shi zarafi yă ji daɗinsu, ya kuma amince da rabonsa, sai yă ji daɗin aikinsa, wannan kyauta ce ta Allah. 20 Da ƙyar yake tunani a kan kwanakin rayuwarsa, domin Allah ya yarje masa, yă zauna da farin ciki.