17
Ruwa daga dutse
Dukan taron Isra’ilawa suka kama tafiya daga Hamadar Sin, suka yi ta tafiya suna sauka a wurare dabam-dabam bisa ga umarnin Ubangiji. A ƙarshe suka sauka a Refidim, suka zauna a can, amma ba ruwan da jama’a za su sha. Saboda haka suka yi wa Musa maganganun banza suka ce, “Ba mu ruwa mu sha.”
Musa ya amsa ya ce, “Don me kuke mini maganganun banza? Don me kuke gwada Ubangiji?”
Amma mutanen suka yi fama da ƙishirwa a can, suka yi gunaguni a kan Musa. Suka ce, “Don me ka fitar da mu daga Masar, ka sa mu da ’ya’yanmu da dabbobinmu, mu mutu da ƙishirwa?”
Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Me zan yi da wannan jama’a? Suna shiri su jajjefe ni da duwatsu.”
Ubangiji amsa wa Musa, “Ka ɗauki sandan da ka bugi ruwan Nilu da shi. Ka kira waɗansu shugabannin Isra’ila, ku wuce a gaban jama’ar. Zan tsaya a can a gabanka, kusa da dutsen Horeb. Ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito daga gare shi domin mutane su sha.” Sai Musa ya yi haka a idon dattawan Isra’ila. Sai suka ba wa wurin suna, Massa da Meriba, saboda Isra’ilawa sun yi jayayya, suka kuma gwada Ubangiji cewa, “Ubangiji yana tsakaninmu ko babu?”
An ci Amalekawa da yaƙi
Amalekawa suka zo, suka yaƙi Isra’ilawa a Refidim. Musa ya ce wa Yoshuwa, “Zaɓi waɗansu mazanmu, ka je ka yaƙi Amalekawa. Gobe zan tsaya a bisa tudu, da sandan Allah a hannuwana.”
10 Sai Yoshuwa ya yaƙi Amalekawa kamar yadda Musa ya umarta, Musa, Haruna da Hur kuwa suka tafi bisa tudu. 11 Muddin hannun Musa yana a miƙe, sai Isra’ilawa su yi ta cin nasara, amma da zarar hannunsa ya sauka, sai Amalekawa su yi ta cin nasara. 12 Sa’ad da hannuwan Musa suka gaji, sai Haruna da Hur suka ɗauki dutse suka sa ya zauna a kai. Sa’an nan su kuma suka tsaya gefe da gefe, suna riƙe da hannuwansa har fāɗuwar rana. 13 Sai Yoshuwa kuwa ya ci nasara a kan Amalekawa da takobi.
14 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka rubuta wannan a cikin littafi, yă zama abin tuni, ka kuma faɗa wa Yoshuwa zan hallaka Amalekawa ƙaƙaf daga duniya.”
15 Musa ya gina bagade, sai ya kira shi Ubangiji shi ne Tutata. 16 Ya ce, “Gama an ɗaga hannuwa sama zuwa kursiyin Ubangiji, Ubangiji zai yaƙi Amalekawa daga tsara zuwa tsara.”