22
Tsarewar mallaka
1 “In mutum ya saci saniya ko tunkiya ya yanka, ko ya sayar, zai biya shanu biyar, a maimakon saniyar da ya sata, ko kuma tumaki huɗu, maimakon tunkiyar da ya sata.
2 “In aka iske ɓarawo yana cikin ƙoƙarin shiga yă yi sata, aka buge shi har ya mutu, to, ba za a nemi alhakin jininsa daga wurin kowa ba;
3 amma in ya faru bayan wayewar gari, to, za a nemi alhakin jinin ɓarawon a hannun wanda ya bugi ɓarawon.
“Ɓarawon da aka kama da abin da ya sata, dole yă yi cikakkiyar ramuwa, amma in ba shi da kome, dole a sayar da shi a biya abin da ya sata.
4 In an sami dabbar, ko saniya, ko jaki, ko tunkiya da ya sata da rai a hannunsa, dole ɓarawon yă biya taran da za a ci shi, sau biyu na kowane ɗaya.
5 “In mutum ya sa dabbobinsa su yi kiwo a fili ko a gonar inabi, ya kuma bar dabbobinsa suka yi ɓarna a cikin gonar wani, sai a sa mai dabbar yă biya tara daga amfanin gonarsa mafi kyau duka.
6 “In gobara ta tashi, ta kuma bazu cikin ƙayayyuwa, har ta cinye tarin hatsi, ko hatsin da ke tsaye, ko dukan gonar, dole wanda ya sa wutar, yă biya taran da aka yanka masa saboda ɓarnan da wutar ta yi.
7 “In mutum ya ba maƙwabcinsa azurfa, ko kaya ajiya, aka kuma sace su daga gidan maƙwabcin, in an kama ɓarawon, sai ɓarawon yă biya abin da ya sata har sau biyu.
8 Amma in ba a sami ɓarawon ba, sai wanda aka yi ajiyar a gidansa, yă bayyana a gaban alƙalai a bincika ko yana da hannu a kan kayan maƙwabcinsa.
9 A kowane rikicin cin amana da zai shiga tsakanin mutum biyu, ko a kan bijimi, ko jaki, ko tunkiya, ko riga, kai, ko a kan kowane irin abin da ya ɓata, da ma abin da aka samu a hannun wani, in akwai jayayya, za a kawo mutumin a gaban alƙalai. Wanda alƙali ya ce shi ne mai laifi, sai yă biya ɗayan taran da za a yanka, har sau biyu.
10 “In mutum ya ba da jaki, ko saniya, ko tunkiya, ko kowace dabba wa maƙwabcinsa ajiya, sai abin ya mutu, ko ya ji rauni, ko an ɗauke shi, in ba shaida,
11 rantsuwa ce za tă raba tsakaninsu a gaban Ubangiji cewa babu hannunsa a dukiyar maƙwabcinsa. Mai dukiyar kuwa zai yarda da rantsuwar, ba za a bukaci wanda aka bai wa amanar yă biya ba.
12 Amma idan satan dabbar ce aka yi, dole wanda aka bai wa ajiyar yă biya mai dabbar taran da aka ci masa.
13 In naman jeji ne ya kashe ta, zai nuna gawar don shaida, ba za a kuwa sa maƙwabcin yă biya abin da naman jeji ya kashe ba.
14 “In mutum ya yi aron dabba daga wurin maƙwabcinsa, sai dabbar ta ji rauni ko ta mutu, yayinda mai shi ba ya nan, dole wanda ya yi aron dabbar yă biya.
15 Amma idan mai dabbar yana a wurin, wanda ya karɓa aron, ba zai biya kome ba. In an yi hayar dabbar ce, to, kuɗin da aka biya na hayar zai zama a madadin rashin.
Hakkin zamantakewa
16 “Idan mutum ya ruɗe budurwa, wadda ba wanda yake nemanta, ya kuma kwanta da ita, dole yă biya kuɗin aurenta, za tă kuma zama matarsa.
17 In mahaifinta ya ƙi yă ba da ita ga mutumin, dole mutumin yă biya dukiya daidai da abin da akan biya domin budurwai.
18 “Kada ku bar maiya da rai.
19 “Duk mutumin da ya yi jima’i da dabba dole a kashe shi.
20 “Duk wanda ya yi hadaya ga wani allah ban da Ubangiji, dole a hallaka shi.
21 “Kada a wulaƙanta, ko a zalunci baƙo, domin dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.
22 “Kada ku ci zalin gwauruwa, ko maraya.
23 In kuka yi haka, idan kuma suka yi kuka gare ni, zan ji kukansu.
24 Zan husata, in kuma kashe ku da takobi; matanku kuma, su ma su zama gwauraye, ’ya’yanku kuwa su zama marayu.
25 “In kun ba wa jama’ata matalauta da suke tsakaninku bashin kuɗi, kada ku zama kamar masu ba da rance; kada ku sa yă biya da ruwa.
26 In kun ɗauki mayafi maƙwabcinku a matsayin jingina, ku mayar masa kafin fāɗuwar rana,
27 domin mayafin ne abin da yake da shi na rufe jikinsa. To, da me zai rufu yă yi barci? Sa’ad da ya yi mini kuka, zan ji, gama ni mai tausayi ne.
28 “Kada ku yi maganar saɓo ga Allah, ko ku la’anta mai mulkin mutanenku.
29 “Kada ku jinkirta fitar da zakarku daga rumbunanku, ko harajin kayan da kuka saya.
“Dole ku ba ni ’ya’yan farinku maza.
30 Ku yi haka da shanunku da tumakinku. Bari su kasance da iyayensu mata, har kwana bakwai, amma ku ba ni su a rana ta takwas.
31 “Za ku kasance mutanena masu tsarki. Saboda kada ku ci naman da namun jeji suka kashe; ku jefa wa karnuka.