30
Bagaden turare
(Fitowa 37.25-28)
1 “Ka yi bagade da itacen ƙirya don ƙona turare.
2 Zai zama murabba’i, tsawon zai zama kamu ɗaya, fāɗi kuma kamu ɗaya, amma tsayin yă zama kamu biyu, ƙahoninsa kuma su zama ɗaya da shi.
3 Ka dalaye bisansa da kuma dukan gefe-gefensa da kuma ƙahoninsa da zinariya zalla, ka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi.
4 Ka yi zobai biyu na zinariya domin bagade a ƙarƙashin zubin, biyu a gefe da gefe su fuskanci juna, don su riƙe sandunan da ake amfani da su don ɗaukarsa.
5 Ka yi sandunan nan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya.
6 Ka sa bagaden a gaban labulen da yake gaban akwatin alkawari, a gaba murfin kafara wanda yake bisa akwatin alkawari, inda zan sadu da kai.
7 “Haruna zai ƙone turare a bisa bagaden kowace safiya, sa’ad da yake shirya fitilu.
8 Dole Haruna yă ƙone turare sa’ad da ya ƙuna fitilu da yamma, ta haka za a riƙa ƙona turare a gaban Ubangiji, daga tsara zuwa tsara.
9 Ba za a ƙona wani irin turare dabam a bisa wannan bagade ba, ba kuma za a miƙa hadaya ta ƙonawa, ko ta hatsi, ko ta sha a bisansa ba.
10 Sau ɗaya a shekara, Haruna zai yi kafara a bisa ƙahoninsa. Dole a yi wannan kafara ta shekara-shekara da jinin kafara ta hadaya don zunubi daga tsara zuwa tsara. Gama bagaden mafi tsarki ne ga Ubangiji.”
Kuɗin kafara
11 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,
12 “Sa’ad da za ku ƙidaya Isra’ilawa, dole kowanne yă biya domin yă fanshe kansa ga Ubangiji a lokacin da aka ƙidaya shi. Ta haka babu wata annobar da za tă buge su sa’ad da kuke ƙidaya su.
13 Kowannen da ya ƙetare zuwa wurin waɗanda aka riga aka ƙidaya, dole yă ba da rabin shekel, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda nauyinsa garwa ashirin ne. Wannan rabin shekel hadaya ce ga Ubangiji.
14 Duk waɗanda suka ƙetare, waɗanda shekarunsu ya kai ashirin ko fiye, za su ba da hadaya ga Ubangiji.
15 Masu arziki ba za su bayar fiye da rabin shekel ba, talakawa kuma ba za su bayar ƙasa da haka ba, sa’ad da za ku yi hadaya ga Ubangiji don kafara rayukanku.
16 Ku karɓi kuɗin kafara daga hannun Isra’ilawa, ku yi amfani da shi domin hidimar Tentin Sujada. Zai zama abin tunawa ga Isra’ilawa a gaban Ubangiji, don su yi kafarar rayukansu.”
Kwano don wanki
(Fitowa 38.8)
17 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,
18 “Ka yi daro na tagulla, ka yi masa ƙafafun da za a ajiye shi da tagulla don wanki. Ka ajiye shi tsakanin Tentin Sujada da bagade, ka zuba ruwa a ciki.
19 Haruna da ’ya’yansa maza za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu da ruwan da yake cikinsa.
20 Duk lokacin da suka shiga Tentin Sujada, za su yi wanka, don kada su mutu. Duk lokacin da suka yi kusa da bagade don hidima ta miƙa hadayar da aka yi wa Ubangiji da wuta,
21 za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu, don kada su mutu. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla domin Haruna da zuriyarsa daga tsara zuwa tsara.”
Man shafewa
(Fitowa 37.29)
22 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,
23 “Ka ɗauki waɗannan kayan yaji masu kyau, shekel 500 na ruwan mur, rabin turaren sinnamon mai daɗin ƙanshi shekel 250, shekel 250 na turaren wuta mai ƙanshi,
24 shekel 500 na kashiya, duk bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, da moɗa na man zaitun.
25 Da waɗannan za ka yi man shafewa mai tsarki, yadda mai yin turare yake yi. Zai zama man shafewa mai tsarki.
26 Sa’an nan ka yi amfani da shi don shafa wa Tentin Sujada, da akwatin alkawari,
27 da tebur da kuma dukan kayansa, da wurin ajiye fitila da dukan kayansa, da bagaden ƙona turare,
28 bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayansa, da daro da mazauninsa.
29 Za ka tsarkake su don su zama mafi tsarki, kuma duk abin da ya taɓa su, zai zama mai tsarki.
30 “Ka shafe Haruna da ’ya’yansa maza, ka kuma tsarkake su don su yi mini hidima a matsayin firistoci.
31 Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Wannan mai, zai zama mai tsarki ne a gare ni don shafewa, daga tsara zuwa tsara.
32 Kada a zuba a jikunan mutane, kada kuma a yi wani mai irinsa. Wannan mai, mai tsarki ne, za ku kuma ɗauke shi a matsayi mai tsarki.
33 Duk wanda ya yi irin wannan mai, duk wanda kuma ya shafa shi a kan wani wanda yake ba firist ba, za a ware shi daga mutanensa.’ ”
Turare
34 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki kayan yaji mai ƙanshi, resin na gum, da onika, da galbanum, da kuma zallan lubban, duk nauyinsu yă zama daidai.
35 Ka yi turare mai ƙanshi yadda mai yin turare yake yi. A sa masa gishiri, yă zama tsabtatacce, tsarkakakke.
36 Ka ɗiba kaɗan daga ciki, ka niƙa, ka ajiye a gaban akwatin alkawari a cikin Tentin Sujada, inda zan sadu da kai. Zai zama mafi tsarki a gare ku.
37 Kada ku yi wani turare irinsa wa kanku; ku ɗauke shi a matsayi mai tsarki ga Ubangiji.
38 Duk wanda ya yi irinsa don jin daɗin ƙanshinsa, dole a ware shi daga mutanensa.”