40
Kafawa tabanakul
1 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,
2 “Ka kafa tabanakul, da Tentin Sujada, a kan rana ta fari ga watan fari.
3 Ka sa akwatin Alkawari a cikinsa, sa’an nan ka rufe shi da labule.
4 Ka shigar da teburin ka shirya kayayyakin a kansa. Sa’an nan ka shigar da wurin ajiye fitilan ka kuma sa fitilunsa.
5 Ka sa bagaden zinariya na ƙona turare a gaban akwatin Alkawari, ka kuma sa labule a ƙofar shiga tabanakul.
6 “Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar tabanakul, da Tentin Sujada;
7 ka ajiye daron tsakanin Tentin Sujada da bagaden, ka kuma zuba ruwa a cikinsa.
8 Ka yi fili kewaye da shi, ka kuma sa labule a ƙofar shiga filin.
9 “Ka ɗauki man shafewa ka shafe tabanakul da duka abin da yake cikinsa; ka keɓe shi da dukan kayayyakinsa, zai zama tsarkake.
10 Sa’an nan ka shafe bagaden hadaya ta ƙonawa da kayansa; ka keɓe bagaden, zai zama mai tsarki.
11 Ka shafe daron da wurin ajiyarsa, ka kuma keɓe su.
12 “Ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka wanke su da ruwa.
13 Sa’an nan ka sa wa Haruna tsarkakun riguna, ka shafe shi, ka kuma keɓe shi don yă yi mini hidima a matsayin firist.
14 Ka kawo ’ya’yansa maza ka sa musu taguwoyi.
15 Ka shafe su yadda ka shafe mahaifinsu, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Shafe musu man, zai sa su zama firistoci na ɗinɗinɗin, dukan zamanansu.”
16 Musa ya aikata dukan kome yadda Ubangiji ya umarce shi.
17 Da haka aka kafa tabanakul, a rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu.
18 Sa’ad da Musa ya kafa tabanakul, ya sa rammuka a wurinsu, ya sa katakan, ya kuma sa sandunan, ya kakkafa dogayen sandunan.
19 Sa’an nan ya shimfiɗa tentin a bisa tabanakul, ya kuma sa murfi a bisa tentin, yadda Ubangiji ya umarce shi.
20 Ya ɗauki dokokin Alkawari ya sa a cikin akwatin, ya kuma zura sandunan a zoban akwatin, sa’an nan ya sa murfin kafara a bisansa.
21 Sai ya kawo akwatin a cikin tabanakul, ya kuma rataye labulen rufewa ya tsare akwatin Alkawarin, yadda Ubangiji ya umarce shi.
22 Musa ya sa teburin a Tentin Sujada, a gefen arewa na tabanakul waje da labulen.
23 Ya shirya burodin a kai a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.
24 Ya sa wurin ajiye fitilan a Tentin Sujada ɗaura da teburin a gefen kudu na tabanakul
25 ya kuma shirya fitilun a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.
26 Musa ya sa bagaden zinariya a cikin Tentin Sujada a gaban labulen
27 ya ƙone turare mai ƙanshi a kai, yadda Ubangiji ya umarce shi.
28 Sa’an nan ya sa labule a ƙofar shiga na tabanakul.
29 Ya sa bagaden hadaya ta ƙonawa kusa da ƙofar tabanakul, Tentin Sujada, sa’an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a kansa, yadda Ubangiji ya umarce shi.
30 Ya sa daro tsakanin Tentin Sujada da bagade, ya kuma zuba ruwa a cikinsa don wanki,
31 a cikin kuwa Musa da Haruna da ’ya’yansa maza sukan wanke hannunsa da ƙafafunsu.
32 Sukan yi wanka a duk sa’ad da suka shiga Tentin Sujada, ko in suka kusaci bagade, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
33 Sa’an nan Musa ya yi fili kewaye da tabanakul da kuma bagaden, ya rataye labule a ƙofar shiga filin. Da haka Musa ya gama aikin.
Ɗaukakar Ubangiji
34 Sa’an nan girgije ya rufe Tentin Sujada sai ɗaukakar Ubangiji ta cika tabanakul.
35 Musa bai iya shiga Tentin Sujada ba domin girgije ya riga ya sauka a kansa, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika tabanakul.
36 Cikin tafiyar Isra’ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa’ad da girgijen ya tashi daga kan tabanakul.
37 Idan girgijen bai tashi ba, ba za su tashi ba, sai a ranar da ya tashi.
38 Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan tabanakul da rana, da dare kuwa wuta yake cikinsa domin dukan Isra’ilawa su gani.